Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ronaldo ya yaba wa Zinedine Zidane

Tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen, dan asalin Fotugal, Cristiano Ronaldo, a shekaranjiya Laraba ne ya yaba wa kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane.  Ya ce a gaskiya Zidane kwararren koci ne wanda ya san yadda yake tafiyar da harkar horarwa da hakan ta sa yake samun nasara.

Zidane dai ya samu nasarar lashe kofunan zakarun kulob na Turai sau uku a jere amma sai ya yi murabus a farkon kakar wasa ta bana.   A watan jiya ne ya sake karbar ragamar horar da Madrid bayan mahukunta Madrid sun din sun lallashe shi.

ADVERTISEMENT

Ronaldo, wanda ya canza sheka zuwa kulob din Jubentus na Italiya, kafin ya bar Madrid ya lashe kofin zakarun kulob na Turai sau hudu, amma uku daga ciki ya yi su ne a karkashin horarwar Zidane.

“Ba kasafai ake samun irin kwarewar da Zidane yake da ita a fagen horarwa ba.  Koci ne da ya san yadda yake tafiyar da ’yan wasansa da hakan ta sa yake samun nasara”, inji shi.

ADVERTISEMENT

Zidane dai ya sake zama kocin Madrid ne a watan jiya bayan kulob din ya fada matsala, sai dai alamu sun nuna mahukunta kulob din za su ba shi makudan kudi don cefano zaratan ’yan kwallo a karshen kakar wasa ta bana.