Da Dumi Dumi

Rouhani ya musanta batun ganawa da Donald Trump

Shugaban Iran Hassan Rohani ya kawar da yiyuwar tattaunawa a tsakanin kasarsa da Amruka, tare da bayyana cewa kamar yadda aka tsara nan da kwana biyu, kasar Iran za ta rage amfani da wani bangare na yarjejeniyar Nukiliyar da ta cimma tsakaninta da kasashen Turai.

Mahukuntan birnin Tehran da wasu kasashen Turai uku da suka hada da Faransa da Jamus da Burtaniya na kokarin ceto yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 da ta tanadi takaita shirin samar da makamashin Nukiliyar Iran, bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar a bara, tare da mayar da jerin takunkumin da Amurkar ta kakaba wa  Iran.

Kwana guda bayan tattaunawar da ta shiga tsakanin kwarrarun kasashen Faransa da Iran a birnin Paris, Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Ybes Le Drian ya ce damar da ake da ita ta son tattaunawa tsakanin Iran da Amuka a cikin gaggawa na ci gaba da kankancewa domin kuwa akwai batutuwa da dama da suka kamata a magance

Wata majiyar diflomasiyar Faransa ta ce, dangane da tattaunawar Nukiliyar za a iya cewa karara Iran ta nuna munanan alamu, idan har ta rage amfani da alkawuran da ta dauka kan aiki da yarjejeniyar Nukiliyar da aka cimma a wannan mako

Idan dai za a iya tunawa a karshen watan jiya ne a taron kasashe bakwai masu karfin tattalin arzikin masana’antu na duniya G7 a Faransa, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka suka bayyana yiyuwar yin wata ganawa a tsakanin Donald Trump da Shugaban Iran Hassan Rouhani.

ADVERTISEMENT
Share