✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rubutacciyar Waƙa (1)

A wannan mako Aminiya ta yi ninkaya ce a cikin kogin fasaha inda muka yi nazari tare da tattaro bincikin masana a fannin adabin baka.…

A wannan mako Aminiya ta yi ninkaya ce a cikin kogin fasaha inda muka yi nazari tare da tattaro bincikin masana a fannin adabin baka. Mun kawo nazari a kan rubutacciyar waka domin amfanin ma’abota wannan shafi da kuma daliban ilimi. Waƙa, wata hanya ce ta isar da saƙo, tana da matuƙar tasiri a harkar adabi. Hanya ce mai sauƙi wajen isar da saƙo cikin nishaɗi. Akwai waƙa da ake rerewa haɗe da kiɗa, akwai rubutacciyar waƙa wacce ake kira waƙe. Wannan rubutun da mai karatu ke karantawa, a kan ta biyun zai yi magana:

 

Ma’anar Waƙa.

A sauƙaƙƙiyar Hausa, ana iya siffanta waƙa da aunanniyar magana, kamar yadda ya zo a Junaidu da ’Yar’aduwa (2002). Ita rubutacciyar waƙa, rubutata ake yi ko da za a rera ta daga baya (Ɗangambo, 1984), sannan tana da ma’auni da sai ta hau kansa kafin ta zama cikakkiyar waƙa.

Rabe-Raben Rubutacciyar Waƙa

Masana sun kasa ta zuwa kashi biyu:

1. Waƙoƙin ƙarni na 19

2. Waƙoƙin ƙarni na 20

Farfesa Ɗangambo (1984), Junaidu da ’Yar’aduwa (2002), Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa (1992), na daga cikin jerin masanan da suka yi tarayya a kan waɗannan rabe-rabe na rubutacciyar waƙa.

Waƙoƙin Ƙarni na 19

Su ne waƙoƙin farko da aka fara rubutawa a Adabin Hausa. Waɗannan waƙoƙi an rubuta su ne cikin rubutun ajami da Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo da almajiransa suka rubuta.

Waƙoƙin Ƙarni na 20

Su ne waƙoƙin da aka rubuta su bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo. Waɗannan waƙoƙi rukuni biyu ne; rukunin farko su ne waɗanda aka ci gaba da rubuta su a cikin ajami kamar waƙoƙin Sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi, da waƙoƙin Aliyu Namangi da sauransu. Sai kuma rukuni na biyu waɗanda aka rubuta su da Hausar boko. A wannan rukuni akwai mawaƙa irin su Sa’adu Zungur, Mu’azu Haɗeja, da kuma Abubakar Ladan.

Tarihin Rubutattun Waƙoƙi

Daga abin da ya gabata na rabe-raben rubutattun waƙoƙin Hausa, muna iya cewa, an fara rubuta waƙa ce cikin harshen Hausa a Karni na 19 a zamanin jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo domin wa’azantarwa. Kuma wannan magana tana iya zama mai ƙarfi idan muka ƙarfafe ta da hujjoji. Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), suka ce, “Rubutacciyar Waƙa ta samo asali ne daga jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, wato a cikin Karni na 18 zuwa Karni na 19.” Sai kuma Farfesa Ɗangambo (1984), da ya ce, “Kamar yadda tarihi ya nuna, rubutattun waƙoƙi na Hausa, sun fi samuwa ne a ƙarni na 19. Ko ma da an samu rubutattun waƙoƙi kafin ƙarni na 19, to, kaɗan ne. Bisa haƙiƙa  waƙa ɗaya ce wadda dai ake da ita a yanzu, ake zaton an yi ta a ƙarni na 17/18, wato “Waƙar Badar,” ta Wali Ɗan Masani na Katsina.”

Nazarin Rubutattun Waƙoƙi

A taƙaice, mai nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa zai lura da abubuwa kamar haka:

1. Jigo: Shi ne saƙon da aka gina tubulin waƙar a kansa. Abin nufi, saƙon da ake son isarwa a waƙar. A kan gina waƙoƙi a kan jigo da suka haɗa da wa’azi, yabon Annabi da waliyayai, soyayya, gargaɗi, siyasa, da sauransu.

2. Zubi da Tsari/Salo: Ana rubuta waƙa ce a layi-layi wanda ake kiran kowane layi guda ɗango. Waɗannan layuka (ɗangwaye) guda biyu zuwa biyar su suke samar abin da ake kira baiti. Ƙarshen kowane ɗango (layi) na kowane baiti a kan so ya ƙare da sauti iri ɗaya, wannan shi ake kira amsa amo ko kuma ƙafiya. Ke nan, salon rubuta waƙa ya bambanta da yadda ake rubutun zube da kuma wasan kwaikwayo. Saboda haka a fagen nazarin waƙa idan aka yi maganar zube ko salo, to ana son manazarci ya lura da yadda mawaƙi ya buɗe waƙarsa. Yawancin waƙoƙin Hausa, mabuɗinsu shi ne addu’a. Misali, idan muka duba baitoci biyun farko na waƙar  ‘Maraba da Soja’ ta Malam Sa’adu Zungur:

‘Mu yi salati da sallamawa,

Ga fiyayyen Annabawa,

Wanda ya shige kwaikwayawa,

Shugaban duka jarumawa,

A gare Shi Muke biɗar fakewa.

Allah ɗai ad da ƙudura,

Mulki, iko, da nasara,

Babu tasiri da sutura,

Ba tsimi, kuma ba dabara,

Sai da ƙarfin Jalla, Mai iyawa.’

Idan muka lura za mu ga cewa baitin farko ya fara ne da salati ga Annabi da kuma yabo gare shi. Sannan sai yabo ga Allah wanda ke ƙunshe da sallamawar dukkan al’amura gare Shi kuma hakan na nufin neman taimakonSa a cikin dukkan al’amura kamar yadda ya zo a biti na biyu. To, wannan nau’i ne na addu’a a waƙa.

Bayan wannan kuma sai ƙarshen waƙar, marufi ke nan. Shi ma abin dubawa ne. Wadansu sukan rufe waƙoƙinsu da addu’a, wadansu da bayyana adireshinsu, wadansu kuma sukan haɗe biyun. Misali, Na’ibi Sulaimanu Wali, ya rufe waƙarsa ta Hawainiya da addu’a da kuma faɗin adireshinsa kamar haka:

‘Na gode Allah nai yabo,

A gare Shi a nan zan dakata.

Tsira da amincin Rabbana,

Ga Rasulu da ya hana yin fuce.

Ko za a cane maka wa ya yi?

Waƙan nan malam sai ka ce.

Na’ibi Wali sunansa ne,

Kuma Kurawa unguwarsu ce.

Tamat, yau waƙata ta cika,

Allah sa mu mu bar son yin fuce.’

Bayan an nazarci mabuɗi da marufin waƙa kuma sai a koma baitocinta, a nan kuma za a lura da ɗangwayen waƙar (layuka), an zuba ta  a baituka bibbiyu ne, uku-uku, hur-huɗu ne, ko biyar-biyar? Ba za a so samun saɓani wajen adadin ɗangwayen da ke samar da baitukan waƙar ba. Sai kuma ƙafiya wato amsa amo, shi ma an fi so ya zama abu guda tun daga farko har ƙarshen baiti. Idan aka lura da waƙar Maraba da Soja ta Malam Sa’adu Zungur, za a ga  cewa a baitin farko, dukkanin ɗangwayen suna ƙarewa ne da sautin wa.

3. Salon Sarrafa Harshe: Salon sarrafa harshe na nufin irin Hausar da aka yi amfani da ita wajen rubuta waƙa da kuma shigo da adon harshe cikin waƙar ta hanyar karin magana, kirari, habaici, kamantawa da sauransu. Yin amfani da sauƙaƙƙiya kuma daidaitaciyyar Hausa shi aka fi so, don waɗannan su za su saka waƙar ta zamo mai sauƙin fahimta da kuma daɗin karantawa ga mai karanta ta.

Bin waɗannan matakai ne zai bai wa manazarci damar sanin inda akalar waƙa ta saka gaba har ya gane saƙon da ke cikin waƙa idan abar lura ce, ko kuma yin kullaliyo da ita da kuma ba ta sunan da ya dace da ita amma ba waƙe ba.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano. Da Zungur A. M. S. (1968). Waƙoƙin Sa’adu Zungur. The Northen Nigerian Publishing Company Ltd, Zariya – Najeriya. Da kuma shafin rumbun ilimi.