✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe gidajen mari: Kada garin gyaran gira a rasa ido

A ’yan kwanakin nan jami’an tsaro suna ta kai samame a gidajen mari da wadansu mutane suka bude domin gyara tarbiyyar yaran da suka kangare…

A ’yan kwanakin nan jami’an tsaro suna ta kai samame a gidajen mari da wadansu mutane suka bude domin gyara tarbiyyar yaran da suka kangare suka gagari iyayensu tare da addabar al’ummarsu.

Hukumomi suna ganin wadannan gidaje suna cin zarafin dan Adam ne saboda yadda suke gudanar da ayyukansu ya saba wa doka, domin sanya wa wadanda ke gidajen mari da kuntata musu da ake yi ya wuce iyaka. Har ma zargin yi wa maza da mata fyade ake yi a irin wadannan gidaje.

Daga cikin irin wadannan gidaje da aka kai samamen har da gidan gyaran tarbiyya na Malam Niga da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna, inda Gwamnan Jihar Kaduna da kansa ya jagoranci jami’an tsaro suka je gidan suka saki wadanda ake tsare da su.

Wannan gida na Malam Niga sananne ne, domin ya kwashe shekaru masu yawa ana wannan aikin a cikinsa, kuma an sha yin hira da shi Malam Niga din a kafafen watsa labarai na ciki da wajen kasar nan, inda yake yin bayanin abubuwan da suke gudanarwa a gidan kuma yakan yi bayanin hanyoyin da za a bi domin magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.

Wata majiya ta bayyana cewa wannan cibiyar horarwa ta Malam Niga tana da rajista daga gwamnati, amma abin mamaki sai ga shi gwamnati tana nuna kamar ba ta san da zaman wurin ba sai a ’yan kwanakin nan da ’yan sanda suka kai samame a irin wannan gida da ke Rigasa.

Sai dai kuma wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa gidajen horon suna wuce iyaka ne a yayin gudanar da ayyukansu, idan haka ne za a iya cewa laifin hukuma ce da ba ta kula da yadda suke gudanar da harkokinsu ta hanyar kai ziyara wuraren a lokuta daban-daban ba.

A cibiyar horo ta Malam Niga baya ga ladabtar da wadanda aka kai su gidan, ana kuma koya musu sana’o’i iri-iri domin idan sun fita su zama mutanen kirki su rika dogara da kansu. Kuma babu wani rahoto da aka samu da ke nuna cewa masu cibiyoyin ne suke kama mutane da karfin tsiya suna daure su, duk wanda aka gani a wurin iyayensa ne suka kai shi domin a hora shi saboda ya gagare su. Kuma ba ’ya’yan talakawa ne kawai a wurin ba har da ’ya’yan manyan mutane.

Yanzu iyaye sun koma su ne ’ya’ya, ’ya’ya kuma sun koma su ne iyaye, domin iyaye suna dawainiya da yaransu da yawa, su ne masu kai su makaranta, su ne masu zuwa su dauko su. Duk wata hidima da yaran suke bukata su ne za su yi musu, yaran suna kwance a daki maigida zai fita ya je ya nemo musu abin da za su ci, ba su taimaka masa da komai. Idan suna makarantar kwana ce ana kashe musu makudan kudi a kuma ba su makudan kudi na kashewa, hakan yana sa yaro  ya shagwabe ya ki yin karatu, maimaikon haka sai ya mayar da hankali wajen shaye-shaye da ayyukan banza saboda yana da kudi.

Saboda yawan gata da ake nuna wa yaran sai suka fi karfin iyayen nasu, har ta kai ga a wani lokacin iyaye suna matukar tsoron ’ya’yansu, domin idan suka yi musu fada ransu zai baci har su yi barazanar kashe su. Sai ka ga yaro yana zaune da iyayensa amma ba ya magana da su, gaisuwar baka ma ta gagara, kuma ya hana kowa sukuni a gidan, matukar yana nan to hankalin kowa da ke gidan a tashe yake. Irin wadannan yaran ne ake kaiwa gidan mari domin a gyara tarbiyyarsu tunda sun zama gagararru.

Ita kanta gwamnati tana da irin wannan gidan gyara tarbiyyar yara a Kakuri da ke Kaduna, a wannan gida ana horar da yara ne idan sun yi hankali sai a koya musu sana’a. Da farko idan an kai yaro gidan ana fara sanya shi a bangare ne mai dakuna horarwa iri-iri (cells) da aka sanya wa dakunan sunayen dabbobin dawa, irin su zaki, damisa, kura da sauran dabbobi da ake tsoronsu a dawa. Bako na shiga wurin da suke irin gaisuwar da za su yi masa ma ta ban tsoro ce, domin gaisuwa suke yi mai kama da yadda wadannan dabbobin suke kuka.

Idan yaro ya yi hankali ne sai a fitar da shi daga wannan bangaren a koma da shi bangaren da ke da wurin kwana irin na daliban makaranta inda za a koya masa karatu da sana’ar da yake so.

Saboda haka maimakon a rufe wadannan gidajen horon kamata ya yi gwamnati ta tallafa musu ta hanyar horar da su yadda ya kamata su gudanar da ayyukansu daidai da zamani, ba a rika cin zarafinsu ana nuna kamar su ’yan ta’adda ne ba. Domin iyayen da ke kai ’ya’yansu suna yabawa da abubuwan da ake yi wa ’ya’yan nasu, hatta wadansu daga cikin wadanda aka kai su gidajen horon suna nuna godiyarsu saboda an dawo da su kan hanya.

Yanzu rufe gidajen da ake yi zai sanya a kara samun kangararrun yara, domin wadanda aka sako su za su koma su hadu da sauran yara su bata su tunda ba su riga sun horu ba aka sako su, kuma an nuna musu cewa su shafaffu ne da mai a wurin gwamnati. Iyayensu da suka kai su gidan horon kuma sun shiga uku a wurin yaran, domin yaran za su ci gaba da gallaza musu saboda sun san babu abin da za su yi musu.

Ya kamata iyaye su kula da tarbiyar ’ya’yansu, domin shagwaba su da suke yi da yawa ne yake sanyawa suke fin karfinsu, a wani lokacin kuma iyaye suna kokari a gida amma sai yaran su hadu da muggan iri a makaranta su lalata musu tarbiyya. Saboda haka da iyaye da malamai, musamman masu makarantun kudi da kuma hukuma sai sun tashi tsaye wajen gyaran tarbiyyar yara idan ana so a samu shugabanni nagari a nan gaba.

Su kuma gidajen marin su yi kokarin su inganta harkokinsu yadda za su tafi daidai da zamani, gwamnati kuma ta rika taimaka musu da kudi da kuma horar da su hanyoyi na zamani, domin taimaka wa gwamnati suke yi wajen inganta tarbiyya, saboda gwamnati ita kadai ba za ta iya ba.