Search
Subscribe
Rufe iyaka: Mutanen Ghana sun rufe shagunan ’yan Najeriya 50 a kasarsu

Rufe iyaka: Mutanen Ghana sun rufe shagunan ’yan Najeriya 50 a kasarsu

Rufe iyaka: Mutanen Ghana sun rufe shagunan ’yan Najeriya 50 a kasarsu

Rufe iyakar Najeriya da makwabtanta na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce  a tsakanin jama’ar Najeriya da na sauran kasashe, inda wadansu ke cewa rufe iyakar ta kawo matsaloli da yawa, wadansu kuma ke cewa matakin ya taimaka wajen hana shigo da kayan ta’addanci da kwayoyi da sauransu. Shakka babu wannan lamari na rufe iyakar Najeriya ya kawo damuwa da matsaloli iri-iri ga direbobi da ’yan kasuwa da matafiya.

Kungiyar ’Yan kasuwa masu dillacin kayayyakin lantarki ta kasar Ghana ta aiwatar da alwashin da ta yi inda ta rufe shaguna 50 na ’yan Najeriya da ke Kasuwar Opera Skuare a tsakiyar Accra, babban birnin kasar.

Kungiyar a makon jiya ta bayar da sanarwar cewa kowane dan kasuwar da ba dan kasar Ghana ba, ya tattara nasa-ya-nasa ya fice daga kasuwar zuwa ranar 4 ga  Nuwamban da muke ciki. Kungiyar ta kuma garkame shagunan ’yan Najeriya a birnin Kumashi.

An ruwaito kakakin kungiyar, Samuel Addo na cewa daukar matakin hakan ya yi daidai da Sashen Dokar Habaka Zuba Jari ta Kasar ta 27 (1)  Doka mai lamba 865, wacce ta yi tanadin cewa duk wani sha’anin kasuwanci na sayarwa kai- tsaye – lallai ne ’yan kasa ne kawai ke da damar yin sa.

An ga yadda mambobin kungiyar suka dirar wa shagunan ’yan Najeriyar a cikin kasuwar da misalin karfe 10 na safe, inda suka umarce su da ficewa daga cikin shagunan nasu tare da garkame su da kwaduna.

Sai dai a lokacin da suke aiwatar da haka, ’yan kasuwar Ghana ba su fuskanci wata turjiya ba daga ’yan kasuwar Najeriyan – wadanda suka mika wuya cikin ruwan sanyi. Sai dai kuma babu jami’an tsaro da suka yi musu rakiya a daidai lokacin da wannan ke faruwa.

Sai dai tun farko, wadansu ’yan Najeriya da suke daukar kansu a zaman ’yan kasa, ta hanyar haifansu a Ghanar, sun roki ’yan Ghana su yi wa Allah da Ma’aikinSa (SAW) su kyale su wajen ci gaba da gudanar da kasuwancinsu a kasar.

Shugaban Kungiyar ’Yan Najeriya da ke kasuwanci a Ghanar, Chukwuemeka Nnaji, wanda yana farfajiyar kasuwar lokacin da ake dirar mikiyar, daga baya ya kai rahoton hakan ga ’yan sandan kasar.

Sai dai babu rahoton samun wani hargitsi a kasuwar ta Opera Skuare har zuwa yammacin ranar Litinin, yayin da harkokin kasuwanci ke ci gaba da gudana cikin tsanaki.

’Yan kasuwar na Ghana sun ce ’yan kasashen waje musamman ’yan Najeriya na gudanar da harkokin kasuwanci ba bisa ka’ida ba.

To amma ’yan kasuwar na Najeriya sun musanta ikrarin na ’yan Ghana.

Ana dai ganin garkame shagunan ba ya rasa nasaba da rufe iyakokin da Najeriya ta yi, al’amarin da ke ci gaba da tunzura wasu kasashen Afirka.

Gwamnatin Ghana ta nemi ’yan kasuwar na Ghana su guji aikata abin da suke yi domin gudun hakan ka iya shafar alakar kasar da Najeriya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake rufe wa ’yan Najeriya shaguna a Ghana. Ko a watan Yuni ma sai da wadansu mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka rufe shagunan ’yan Najeriya 20 a birnin Kumasi. An kuma samu faruwar irin wannan al’amarin a birnin Accra.

Kungiyar ’yan kasuwa ’yan Najeriyar mazauna Ghana ta bukaci ’yan uwansu su kwantar da hankalinsu inda ta ce tana bakin kokarinta wajen warware matsalar.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin