✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe kan iyaka: An yi kasuwar shinkafa mafi girma a tarihi a Gombe

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekarar nan masu zazzabar shinkafa a garin Gombe sun ce sun yi kasuwar da ba su taba yi…

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekarar nan masu zazzabar shinkafa a garin Gombe sun ce sun yi kasuwar da ba su taba yi ba a tarihi.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya samu jinjina sosai bisa rufe kan iyakar kasa da ya yi wanda hakan ne ya sa aka bunkasa noman shinkafar gida da masu zazzabar ta suke samun kudi masu kyau.

Alhaji Musa Arab, wani mai zazzabar shinkafa a Gombe ya shaida wa Aminiya cewa ya samu cinikin da bai taba tsammani ba daga farkon wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekarar nan da ake ciki.

A cewarsa, gabanin rufe kan iyakar, hakan bai faruwa sai da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya sa aka rufe kan iyakar ya kuma bada umurnin a bai wa manoman rance.

“Hakan ne ya bunkasa harkar noma da bada bashi ga manoman; kuma rufe kan iyakokin ya karfafa wa kananan manoma na cikin gida da ’yan kasuwa,” Kamar yadda ya fada.

Alhaji Musa Arab, ya kuma ce inda ake zazzabar shinkafa yanzu suna loda tirela 20 a kullum kuma suna sarrafa buhuna dubu 15; wanda a baya ba haka abun yake ba.

“Kamar yadda kake gani gwamnatocin jihohin kudancin Najeriya suna bamu kwangilar kai musu buhunan shinkafa yar gida zuwa jihohinsu, yanzu haka gwamnatocin jihohi da dama suna sayen shinkafar daga wajenmu,” inji shi.

Haka kamfanoni da daidaikum mutane suna aiko bukata ta musamman da hakan yake kara mana kwarin gwiwar wannan harka.

Arab, ya roki Shugaban Buhari, da ya tabbatar an samu maslaha ta dindin din na hana fasa kwabrin shinkafa zuwa cikin kasar nan bayan an sake bude kan iyakokin kasar, sannan ya ce shinkafarmu ta gida za ta isa ta wadatar da al’ummar Najeriya.

Wani abun mamaki ya ce bai tashi sanin noman shinkafa yana da muhimmanci ba sai da aka rufe kan iyakar Najeriya.

Da yake jinjina wa Shugaba Buhari na habaka noman shinkafa, ya ce yana tsoron rashin sayen shinkafar zai mayar da hannun agogo baya idan aka sake bude kan iyakokin.

Daga nan sai ya shawarci Gwamnatin Tarayya da cewa a tsaurara tsaro kan iyakokin, koda an sake bude su; saboda masu fasa kwabrin suna ta kokarin ganin sun gurgunta harkar a duk lokacin da aka sake bude kan iyakokin.