✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe kan iyaka: Jihar Gombe za ta iya wadatar da Najeriya da shinkafa – Dukku

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN), reshen Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, ya ce shinkafar da ake nomawa a jihar kadai za ta…

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN), reshen Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, ya ce shinkafar da ake nomawa a jihar kadai za ta iya wadatar da Najeriya.

Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, ya bayyana haka ne a Gombe lokacin da yake zantawa da Aminiya inda ya ce rufe kan iyakar Najeriya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi na hana shigowa da shinkafar kasar waje ba zai shafi jihar ba, domin shinkafar da ake nomawa a Jihar Gombe za ta iya wadatar da kasar nan.

Ya ce da inda ba a noma shinkafa ma misali a lokacin rani; yanzu suna nomawa domin kusan ko’ina a jihar ana noma shinkafar.

Shugaban na RIFAN, ya kara da cewa a shekarun baya a madatsun ruwa na Dadinkowa da Balanga ne kadai ake noma shinkafar a Jihar Gombe; amma yanzu tun daga Kogin Gomben Abba zuwa Wawa, da Kundu da Hashidu da Malala har zuwa Zaune ya kai Jamari duk suna noma shinkafa maimakon yalo da suke nomawa a da.

Ahmed Dukku, ya ce saboda noman shinkafa da ake yi a Jihar Gombe, yanzu kamfanonin sarrafa shinkafa kullum kara zuwa Gombe suke yi.

Ya ce “Akwai Indiyawa da suka zo Gombe daga Kamfanin Orlam da shinkafar da suke saya daga Gombe su kai Argungu a Jihar Kebbi, kullum tana kai tirela 40. Suna kaiwa kamfanin sarrafa shinkafar da babu kamarsa a Najeriya, da ba a noma shinkafa a jihar nan yaya za a yi a samu tirela 40 kullum.”

Ya ce duk noman da aka ce ana yi a Kebbi magana ce kawai bai kai na Gombe ba, tunda daga Gombe ake kai shinkafa Kebbi a kullum.

Ya ce a matsayinsa na Shugaban NECAS na Jihar Gombe su suka fara bada tallafin noman ridi da dawa da sauransu baya ga noman shinkafar.

Batun adadin kadadar da manoman shinkafa suke nomawa a Gombe kuwa, Alhaji Ahmed Dukku, ya ce ba zai iya kayyadewa ba; amma dai ya san a NECAS kadai sun bai wa manoma kadada dubu 160.

Har ila yau, ya ce matsalar manoman shinkafa a Gombe ita ce ta farashi, domin a lokacin girbi buhun bai wuce Naira 6,500 maimakon Naira tara ko dubu 10.

Sai ya yi kira ga gwamnati cewa, tunda noma ya inganta, ta samar da injunan sarrafa shinkafa na zamani don gyara ta ta zama kamar ta waje a cire duwatsu da sauran dauda, saboda yanzu Najeriya za ta iya dogara da kanta ta hanyar noman shinkafa.