✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruftawar gada ta raba al’ummar Dakwa da yankin Abuja

Al’ummar Dakwa da ke yankin Birnin Tarayya Abuja sun samu kansu a cikin mawuyacin hali bayan yankewar zirga-zirga a tsakaninsu da sauran al’ummomin birnin bayan…

Al’ummar Dakwa da ke yankin Birnin Tarayya Abuja sun samu kansu a cikin mawuyacin hali bayan yankewar zirga-zirga a tsakaninsu da sauran al’ummomin birnin bayan wata gada da ta sada su da garin Deidei da suke fita ko dawowa garin ta karye ta yadda ba dama mota ta bi ta hanyar.

Wakilinmu ya ziyarci wajen, inda ya zanta da mazauna garin wadanda suka bayyana cewa hakan na jawo musu tsaiko lokacin fita ko dawowa daga ayyukansu na yau da kullum kasancewar ba dama su bi ta hanyar duk da kusancin da take da shi a a kan wadda ta bi ta garin Madalla da ke Jihar Neja.

A dalilin matsalar masu ababan hawa irin Keke NAPEP da babura ne kadai suke kasadar rabawa ta ragowar hanya da ta rage daga jikin gadar da ruwa ke ci gaba da ci.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa gadar wadda ke daura da wani rukunin gidaje da aka fi sani da suna Police Estate cikon gefenta ne ruwa ya zaizaye kasancewar ruwan rafi da ke bi ta karkashin gadar ya fi karfinta kuma sakamakon haka sai ya yi wa kansa karin hanya inda cikon gefen gadar ya zaizaye.

A zantawarsa da Aminiya, Sarkin Dakwa Dokta Alhassan Musa Baba Chukuri ya ce ruwan rafin da ya ratsa ta gadar na tahowa ne daga wata madatsar ruwa da ke yankin Kwafa a Jihar Neja yayin da wani bangarensa kuma ke saukowa daga kan tsaunin da ke kusa da wajen.

Sarkin Dakwa ya ce mako daya da ya gabata, wani ayarin wakilan Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ziyarci wajen don gane wa idanunsa lamarin wanda ya faru kamar mako uku ke nan yanzu.

Dokta Alhassan Babachukuri ya roki gwamnati ta taimaka wajen gyara gadar kasancewar ta shafi yara ’yan makaranta da mata da ke zuwa asibiti, baya ga ma’aikata da kuma ’yan kasuwa da ke bukatar bi ta hanyar a kullum. Haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gina babbar gadar sama ta mota a tsakanin garin Dakwa da garin Madalla da ke kan titin Zuba zuwa Kaduna, don magance haddura da ke aukuwa a kan mahadar titin wanda ya ce ke cin rayuka a kai-a kai.