Da Dumi Dumi

Ruftawar gini ya kashe uwa da yara 3 a Legas

An tabbatar da mutuwar mutum hudu wadanda suka hada da uwa da yara uku a wani gida da ya rufta a unguwar Magodo Phase I cikin jihar Legas a safiyar yau Asabar.

Darakta Janar na Hukumar bayar da agaji ta (LASEMA), Dakta Olufemi Oke-Osanyitolu, ne bayyanawa majiyarmu hakan a yau Asabar.

Dakta Olufemi, ya kara da cewa ruftawar ginin ya faru ne a gida mai lamba 48 layin Orisha Water Front Otun Araromi, a unguwar Magodo Phase I.

A cewar Hukumar LASEMA, ginin yana saman wani tsauni ne inda ya rufta kan uwa da ‘ya’yanta biyu da kanwarta wanda hakan ya yi sanadiyar ajalin su.

ADVERTISEMENT
Share