Da Dumi Dumi

Ruga: Ba gudu ba ja da baya – Ministan Gona

Ruga: Ba gudu ba ja da baya – Ministan Gona

Ministan Aikin Gona da Raya Karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya ce ana samun kaso mai tsoka na arzikin kasa daga bangaren kiwon dabbobi, amma saboda siyasar da aka sanya ana neman kashe bangaren kiwon dabbobin.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Cibiyar Bincike da Bunkasa Kiwon Dabbobi ta Kasa (NAPRI) da ke Jami’ar Ahamdu Bello a Zariya don gane wa idonsa irin aikace-aikacen cibiyar.

Ministan ya ce babu gudu ba ja da baya game da batun samar da matsugunan makiyaya a kasar nan.

Alhaji  Sabo Nanono ya bayyana cewa ’yan Najeriya suna kiwon dabbobi da kudinsu ya kai sama da Naira tiriliyan 30,wanda ya kamata a ce ana kula da su domin amfanin kasa.

Ya ce rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa akwai shanu sama da miliyan 20 da dimbin awaki da tumaki, da aladu da jakuna da dawaki, wadanda a cewarsa idan aka yi kiyasin kudinsu sun haura Naira tiriliyan 30, wanda hakan dukiya ce ga kasa.

ADVERTISEMENT

Don haka sai Ministan ya shawarci ’yan Najeriya su cire siyasa a sha’anin aikin gona domin bai wa bangaren damar ba da gudunmawa wajen samar wa kasa da kudin shiga domin samun karuwar arziki.

Alhaji Sabo Nanono, ya kalubalanci masu ilimi da ke harkar aikin gona da kiwo su fito su kare bangaren da aka sanya mummunar siyasa a cikinsa, maimakon su zura wa gwamnati ita kadai ido tana magana.

Ministan ya ce Cibiyar NAPRI da ke Shika tana wanzuwa ce saboda akwai shanu da dawaki da aladu da jakuna da sauransu, don haka sai ya nanata cewa tana da muhimmanci wajen ci gaban kasa.

Ministan ya ce rikici tsakanin manoma da makiyaya tsohon batu ne da ya kai sama da shakara 200.

Ya tuna cewa a zamanin da duk lokacin da aka samu rikicin shugabannin al’umma sukan gano musabbabin rikicin domin magance shi.

Alhaji Sabo Nanono ya nuna takaicin cewa duk da irin ci gaban da aka samu, musamman ta fuskar fasahar zamani amma rikicin sai kara ta’azzara yake yi.

Ya bayyana cewa kiwon dabbobi ya samar da dimbin amfani, inda bangarori da dama da suka hada da mahauta da masu sufuri da ’yan kasuwa suke amfana.

Da yake jawabin maraba, Babban Daraktan Cibiyar NAPRI, Farfesa Clarance Lakpini ya ce an kafa cibiyar ce a 1928 a matsayin wurin tara shanu domin a yi bayensu, inda kuma a ranar 1 ga watan Yunin 1976 ta zama cikakkiyar cibiyar bincike.

Ya bayyana cewa babban aikin cibiyar shi ne gudanar da bincike a kan yadda za a bunkasa kiwon dabbobi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya