✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruguntsumin Sallah

A ranar Talata da ta gabata ce aka gudanar da bukukuwan Karamar Sallah a Najeriya, bayan sanarwar da mai martaba Sarkin Musulmi ya gabatar a…

A ranar Talata da ta gabata ce aka gudanar da bukukuwan Karamar Sallah a Najeriya, bayan sanarwar da mai martaba Sarkin Musulmi ya gabatar a ranar Lititin da ta gabata, na ganin watan Shawwal na bana. Wakilanmu daga sassa daban-daban na Najeriya sun tattaro mana rahotannin yadda aka gudanar da shagulgulan Sallar:

 

A Kano: An fara batun dakatar da Sarki Sanusi

Daga Yusha’u A. Ibrahim, Kano

Sabanin hasashen da aka yi dangane da shagulgulan Karamar Sallah, a Kanon Dabo, miliyoyin Musulmi sun gudanar da bikin na Sallah cikin walwala da annashuwa da wadata.

Kodayake a wayewar washegarin Sallah, Larabar da ta gabata, an wayi gari da labarin da ke cewa akwai yiwuwar dakatar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta, har sai Hukumar Yaki Da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta kammala binciken badakalar kudi a masarautar ta Kano. Shugaban Hukumar ne, Barista Muhyi Magaji ya fitar da rahoto, inda yake shawartar Gwamnatin Jihar Kano da ta dauki wannan mataki.

Kafin ranar Sallah, mutane da dama sun tsammaci za sami gudanar da bikin Sallar cikin kunci saboda rashin kudi a hannun mutane. Sai dai sabanin haka, Musulmi sun gudanar da bikin cikin farinciki sakamakon samin sukunin gabatar da bukatunsu ciki har da girke-girken abincin Sallah da dinkunan sabbin kayan sakawa domin bukukuwan Sallar.

A Unguwannin da Aminiya ta zagaya domin ganin yadda aka gudanar da bukukuwan Sallar kamar Badawa, Gyadi-Gyadi, Tarauni, ’Yankaba, Fagge, Tukuntawa da Tudun Murtala, ya nuna cewa an gudanar da bikin Sallar cikin annashuwa da walwala kuma cikin wadata.

A duk inda ka zaga ka ga yara maza da mata suna karakaina, dauke da abincin Sallah domin kai wa gidajen ’yan uwa da abokan arziki da makwabta, kamar yadda addini ya tanadar. Haka kumasudaiwadananyarannasanye ne da sabbin kaya wanda haka ke nuna cewa Musulmi sun gudanar da bikin na Salla ne cikin wadata.

Malam Ibrahim Yusuf Gyadi-Gyadi ya shaida wa Aminiya cewa, “ni kam Alhamdu lillah, domin kuwa na samu sukunin dinka wa yarana kayan Sallah kuma na dafa abincin Sallah kamar yadda na saba a shekarun baya. Amma gaskiya kimanin nako biyu kafin Sallah, ban yi tsammanin zan dafa abincin Sallah ba duk da cewa na dinka wa yarana kayan Sallah, domin a gaskiya ba ni da kudi a daidai wannan lokacin.

“Amma Allah cikin ikonSa sai wani aikin gini ya fado min wanda bayan na kammala na sami kudin da na sayi shinkafar danya kuma na yi cefanena, kai har ma na sayi naman miya. Don haka ni na gode wa Allah. Ina fatan Allah Ya maimaita mana ta badin badada lafiya.”

Shi ma Alhaji Auwalu Musa Badawa ya shida wa Aminiya cewa shi kam Sallar bana sai hamdala. “Na yi wa yarana dinkin Sallah har kala biyu, da su da mahaifiyarsu. Haka kuma na yi abincin Sallah gami da dan kashin miya. Wannan Sallar ba kamar ta bara ba, domin a bara ban samu sukunin yin haka ba.”

Hajiya Halima Yakubu, wata baiwar Allah da ta tattauna da Aminiya a Gidan Namun Daji na Kano, ta bayyana cewa ta je Gidan Zu ne domin kashe kwarkwatar idanunta. Ta kara da cewa “Duk shekara sai na zo domin kallon namun daji kuma Alhamdu lillah, abin ya kawatar ainun, domin na zagaya cikin gidan namun dajin na yi kallo.

“Na kawo yarana biyu domin su ma su sha kallo kuma sakamakon tattaunawa ta da su na fahimci abin ya kayatar da su. A da can tare da mahaifinsu muke zuwa amma sakamakon yanayin aikinsa, bana bai samu damar zuwa ba don haka ya kawo Naira 800 ya ba ni ya ce mu zo mu yi kallo. Sai dai ya shardanta min cewa lallai in na koma sai na ba shi labarin abubuwan da muka gani kuma na dauki alkawarin da yardarm Ubangiji zan cika wannan alkawarin.”

Aminya ta leka gidan wasannin yara da ake kira Rody da ke kan Titin Ahamadu Bello. A nan ma wakilin namu ya iske yara da yawa suna gudanar da wasanni kala-kala. Shi Rody waje ne da aka kawata shi da abubuwan jan hankalin yara da kuma kayan wasa kala-kala kamar su lilo mai juyawa da lilo mai shillawa da mutum-mutumin namun daji daban-daban amma na roba wadanda yara ke hawa domin wasa.

Wata yarinya mai suna Khadija Isa Bello, ta shaida wa wakilinmu cewa wannan shi ne zuwan ta na farko wurin kuma ita kam kwalliya ta biya kudin sabulu domin abubuwan da aka shirya a gidan sun burge ta gaya.

A Zariya: Jami’an tsaro sun hana ’yan Shi’a Idi  a Litinin

Daga Aliyu Babankarfi Zariya

Wakilinmu ya shaida yadda mabiya Shi’a Zakzakiyya suka yi yunkurin gudanar da Sallar Idi a ranar Litinin da ta gabata, amma sai hakan ba ta samu ba a sakamakon yadda gangamin hadin gwiwar jami’an tsaro a karkashin jagorancin Mataimakin Kwanishinan ’yan sanda a Jihar Kaduna, Sirajo Muhammed Fana mai kula da shiyya ta daya suka gudanar a birnin Zariya da kewaye a ranakun Lahadi da Litinin. Jami’an tsaron sun shiga lungu-lungu cikin zagayen nasu har da wasu wurare da ’yan kungiyar na Shi’a a karkashin jagorancin Ibrahim Yakubu Elzazzaky suka mallaka a da kafin Gwamanatin Jihar Kaduna ta haramta, tare da hana kungiyar gudanar da duk wani al’amari a jihar.

Bikin Karamar Sallah na bana a birnin Zazzau ya gudana a Talata kamar sauran wurare, inda dinbin jama’a suka gudanar da Idi, sannan suka biyo da sauran shagulgula na al’ada.

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris tare da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed el-Rufa’i da dubban al’umma ne suka halarci Sallar a Masallacin Idi da ke Kofar Doka Zariya, inda nayan kammala Sallah sai babban limamin Zazzau, Imam Dalhatu Kasim ya gabatar da huduba a kan yadda Musulmi za su rika gudanar da al’amuransu kamar yadda addininsu ya karantar.

“Wannan rana ce ta farin ciki da murna da annashuwa ga wadanda suka yi koyi da fiyayyan halita, kuma suka gudanar da azumin watan Ramadan na kwana 29 ko 30 kuma wannan rana ce ta farin ciki da kyautata wa marayu, da talakawa da kuma miskinai,” inji limamin.

Da yake mika gaisuwar Sallah ga al’ummar Jihar Kaduna, el-Rufa’i ya mika godiyarsa ga masarautar Zazzau a kan goyon bayan da ake ba su kuma ya sha alwashin kara daukar matakan tsaro, tare da ci gaba da gyaran makarantu da asibitoci domin inganta rayuwar al’umma.

Bayan nan mai sarkin ya yi hawan bikin Sallah daga Kofar Kuyanbana har zuwa fadarsa a kan keken doki, a inda daga bisani Gwamna da Sarki suka zauna domin kallon hawan Sallah da hakimai da ’ya’yan sarki ke yi.

A jawabinsa a yayin bikin Sallar, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi jawabi. “Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa manoma wadataccen takin zamani kuma a farashi mai sauki domin wadata kasa da abinci” inji sarkin.Ya kuma yi kira ga manoma da su kara himma wajen noman kayan abinci da na kasuwanci irin su gyada da auduga da dai sauransu. Ya kuma roki talakawa da su ba gwamnati hadin kai tare da jami’an tsaro da sa ido wajen bayyana duk wani abu wanda ba su yarda da shi ba. Daga karshe ya yi fatan Allah Ya ba da damina mai albarka da zaman lafiya da karuwar arziki a kasa.

A Kafanchan: Sarkin Jama’a ya yaba wa Shugaban Kasa

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Mai martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya yaba da irin matakan tsaron da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake bai wa yankin, wanda hakan ya taimaka wajen samun ci gaba da zaman lafiya.

Sarkin, ya bayyana haka ne a cikin sakon bikin Karamar Sallah a kofar fadarsa da ke garin Kafanchan, jim kadan da dawowa daga Sallar Idin da aka gudanar a babban Masallacin Idi da ke Hayin-Gada, inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron goyon baya tare da zama ’yan kasa nagari masu bin doka da oda. Ya mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kaduna, kan matakan gyara harkokin ilmi tun daga matakin farko a jihar. Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya taimaka ya gyara babbar hanyar da ta taso daga Maraban Kagoro da ke Karamar Hukumar Kaura ta ratso ta garin Kafanchan zuwa Kwoi wacce ta zarce har zuwa Abuja wacce kuma manyan motoci ke yawan bi ta hanyar.

A karshe sarkin ya mika godiyarsa ga jama’arsa da suka nuna halin dattaku da ’yan uwantaka a lokacin gudanar da zabubbukan gwamnoni da na Shugaban Kasa da ya gabata, duk da irin bambamce-bambamcen ra’ayin siyasa da ke akwai a tsakaninsu, inda aka gama lafiya ba tare da samun wani rikici ba. Sannan ya yi kira ga jama’a da su bai wa zababbunsu goyon baya don gudanar da ayyukan ci gaba a yankin baki daya.

A Gombe: Gwamna Inuwa ya nemi a zauna lafiya

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Al’ummar Jihar Gombe sun bi sahun Musulman duniya wajen gudanar da bikin Sallar Idi, bayan kawo karshen azumin Ramadan.

Bayan idar da Sallar mai raka’a biyu da babban limamin Gombe, Alhaji Pindiga ya jagoranta, sai tawagar Gwamnan Jihar, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ta zarce zuwa Gidan Gwamnatin jihar tare da jiga-jigan ’yan siyasa don cin abinci kafin a wuce fadar sarki don kallon hawan Sallah.

A jawabinsa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya hori al’ummar Musulmi a jihar da su zauna lafiya da juna. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya karbi ibadar da aka yi, kana ya ja hankalin Musulmi da su yi koyi da darussan da suka koya a cikin watan Ramadan.

Shi kuwa Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III, kira ya yi da a zauna lafiya, musamman tsakanin manoma da makiyaya. Ya kuma bukaci mutane su zama masu bin doka da oda, kar su zama masu daukar doka a hannunsu.

Mahaya dawakai sun yi hawan Sallah da suka burge gwamnan da sarki da sauran ’yan kallo.

A Katsina: Bana ba a yi hawan Sallah ba

Daga Ahmed Kabir S/kuka, Katsina

A Jihar Katsina, duk da sanarwar da masarautun Katsina da Daura suka bayara kan cewa ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba bayan kammala azumin watan Ramadan domin nuna alhini a kan irin yadda ake kai wa al’ummomi hare-hare da satar shanu da kuma garkuwa da mutane, a wasu lokutan ma har da kisan ba gaira ba dalili, hakan bai hana jama’a yin tururuwa ba zuwa masallcin Idi; domin gabatar Sallah.

Dukkan masallatan da aka gudanar da sallolin, an yi addu’o’i na musamman domin neman samun sauki tare da neman kawar da wadannan bala’o’in da ke addabar Arewa da kasa baki daya.

Duk da rashin hawan Salla da aka saba yi, hakan bai hana al’umma yin ado da kai ziyarce-ziyarce a gidajen ’yan uwa da abokan arziki ba, gami da yin kananan wasanni na nishadantarwa, musamman ga yara, kamar irin su hawan kekuna, lilo da sauransu. Kuma garin na Katsina ya cika da baki sosai, ga kuma yawaitar ababen hawa.

Sai dai kuma akwai jami’an tsaro da ke sanya idanu a kan irin yadda al’amura ke tafiya.

Daga yankin Batsari kuwa, ’yankin da ke fama da hare-haren ta’addanci, ba a samu wata barazana ba, a lokacin da ake cikin bukukuwan Sallar. Alhaji Ali Liman wanda ya jagoranci Sallar Idi a garin, a hudubarsa a masallacin Idi na Izala da ke garin na Batsari, ya ce matakin da Sarkin Katsina ya dauka na soke hawan Sallah ya yi daidai kuma wannan ya nuna sarkin yana tare da jama’arsa.

Kusan duk wadanda Aminiya ta tuntuba a garin na Batsari, sun ce ana ci gaba da harkokin yau da kullum, babu wata matsala. Hatta daga kauyukan da ke gefen garin, inda suke fuskantar barazanar kawo masu hari, komai na tafiya daidai.

A Karamar Hukumar Jibiya kuwa, Aminiya ta jiyo daga bakin Sakataren Kungiyar Makaranta Allo, Malam Lawal Nameri yana cewa: “Gaskiya ana ci gaba da bukukuwan Sallah lami lafiya, babu inda muka ji labarin faruwar wani abu. Irin wannan labarin ne yake fitowa daga Karamar Hukumar Safana ma.”

A shiyyar Daura kuwa, Sarkin Daura Farouk Umar Farouk, tara malamai da hakimai da magaddan masarautar ya yi a fadarsa, bayan an taso daga Sallar Idi, don yin addu’o’i na musamman a kan neman sauki daga Allah a kan masifu da ke addabar Arewa da kasa baki dayanta. An kuma yi addu’o’in Allah Ya bayyanar da Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba a raye cikin ƙoshin lafiya.

Jami’an tsaro sun ba da kulawa wajen gudanar da Sallar Idin. Jama’ar gari sun ci gaba da harkokinsu.

 

A Sakkwato: An nemi Tambuwal ya sanya dokar ta baci kan muhalli

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce ba karamar nasara ce aka samu ba, da malamai da alarammomi suka gudanar da Tafsirin watan Ramadan, wajen fadakar da al’ummar Musulmi hakkokin da ke rataye a wuyansu. Kuma kowa ya koma gidansa lafiya. Sarkin ya bayyana haka ne a jawabinsa na barka da Sallah ga al’ummar Najeriya.

Sarkin ya yi jawabin ne a fadarsa, inda ya ce suna yi wa al’umma godiya don ci gaba da addu’o’in da ake wa shugabanni. “Muna bukatar duk inda aka ga mun yi kuskure a fada mana mu gyara. Kuma tun daga gwamna da mukarrabansa, shugabannin siyasa da duk wani mairi ke da kowane irin mukami ne, domin yin hakan shi ne zai kawo ci gaba.”

Dangane da matsalar ta’addanci da ake fama da ita a wasu jihohin kasar nan, sarkin ya ce “wannan abin bakin ciki ne gare mu, ganin yadda mutane da yawa ba su gidajensu, an kore su. Don haka akwai bukatar shugabannin su hada karfi da karfe domin shawo kan matsalar, al’umma na cikin damuwa kan abin da yake faruwa. Saboda haka sai a dage da addu’a don ba abin da ya gagari Allah.”

Aminiya ta zanta da wasu al’umma a Sakkwato dangane da jawabin Sarkin Musulmi a Sallar bana. Umar Bello ya ce “Jawabin Sarkin Musulmi a karon nan, na yi mamaki yadda bai yi magana a kan muhalli ba, ganin yadda shara (bola) ta cika garin nan, ko’ina kamar garin da ba jagoranci. Ina kira ga Gwamna Tambuwal ya sanya dokar ta baci kan tsabtace muhalli a jihar nan.”

Kabiru Muhammad dan shekara 32 ya ce: “Gaskiya jawabin Sarkin Musulmi ya burge ni matuka, abin da na ga ya rage guda ne, kira ga Gwamna Tambuwal ya dauki mataki kan muhali a birnin jiha, tafi Titin Mai Tuta zuwa Tudunwada da Minanata da Mai Kahon Karo da dukkan titunan da suka zagaye babbar kasuwar Sakkwato, shara ce mai muni a wuraren, kuma hakan kan iya haddasa cututtuka a tsakaninal’umma.

Maryam Abubakar ta ce ana so yayin magana kan bola da ta addabi jihar, “muhallinmu ya baci, ko’ina birnin Sakkwato za ka samu kazanta; kowa yana zuba shara inda yake so. Babu wani mataki da aka dauka a kan wannan lamari.”