✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rumbun makaman Amosun

A ranar Talata 25 ga watan Yuni ne Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun Bashir Makama ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Ibikunle Amosun…

A ranar Talata 25 ga watan Yuni ne Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun Bashir Makama ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Ibikunle Amosun ya mika musu harsasan da suka kai milyan daya da dubu 400 da sauran makamai da kuma hulunan kwano. Makama ya ce yana aiki da hurumin doka da ya ba shi na tabbatar da cewa ya karbi duk wasu makamai da suke a hannun tsohon Gwamna kafin wa’adin gama mulkinsa ya cika a matsayin Gwamnan Jihar. Kwamishinan ya ci gaba da cewa bayanan da Rundunar ’Yan sanda suke da shi a wurinsu ya tabbatar da cewa  Amosun a matsayinsa na Gwamnan Jihar Ogun a shekarar 2012 ya mika bindigogi 1, 000 kirar AK47 amma kuma sai ga shi ya musanta ya taba ganin wani makami a lokacin da suke son su karbi ragowar da suke hannunsa.

Kamar yadda Kwamishinan ya ci gaba da bayani cewa Hedkwatar Rundunar ’Yan sanda ta Kasa tana sane da karbar wadannan makamai. Ya ce “Ba wani abu ne da nake nuku-nukunsa ba, domin ba kayana ba ne, kuma ba kyautarsu ya ba ni ba. Ba kuma cewa ya yi ‘Makama karbi na ba ka kyauta ba.’ Don haka makaman suna nan a ajiye a rumbunmun makamai, yaushe ne za mu yi amfani da su wannan kuma sai mun yi shawara.”

Idan za a iya tunawa tsohon Gwamna Amosun wanda a halin yanzu Sanata ne mai wakiltar Ogun ta Tsakiya a daren jajibirin mika mulki ga wanda ya gaje shi, ya tuntubi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bashir Makama inda ya fada masa cewa akwai wasu makamai da yake da su a gidan gwamnati wadanda yake son mika wa ’yan sanda. A wajen bukin mika makaman ne Amosun ya ce ya yi haka ne domin yana kokarin katange yaduwar matsalar tsaro a cikin jihar. Amosun ya ce ya ajiye su ne a rumbun tara makamai na gidan gwamnati sannan kuma ya hana a ba da su ga kowa koda kuwa jami’in tsaro ne.

Makonni hudu bayan mika wadannan makamai lamarin ya jefa da yawa daga cikin jami’an tsaro da sauran mutane cikin mamakin irin yadda Gwamnan farar hula zai yi rumbu na wadannan dumbin makamai. Ganin cewa ko dokar mallakar makamai ta kasa cewa ta yi ajiye makamai masu yawa dole sai jami’n tsaron da doka ta ba su ikon yin haka  ko kuma wadansu masu lasisin cinikayyar makamai. A haka kuwa babu wani sashe na wannan doka da ya sa Amosun ko kuma Jiharsa daya daga cikin wadanda dokar ta lamunce mawa. Sannan kuma Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ne kawai ke da alhakin ba da irin wannan lasisi.

Da yake amsa tambayoyi game da zargin da ake wa Ibikunle Amosun cewa ya mallaki makamai ba bisa ka’ida ba, Kakakin  tsohon Gwamnan, Rotimi Durojaiye cewa ya yi gwamnatin Jihar Ogun ta samu cikakken lasisi daga gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan ya kuma nuna lambar lasisin wato 000001123 wanda aka sanya wa hannu a ranar 5 ga Mayun shekarar 2012 wanda kuma ya karbo daga Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro. Durujaiye ya ci gaba da cewa don haka ya zama abin dariya da ake yada cewa wai Amosun ya yi sauri ne ya ba ’yan sanda makaman don kada sabuwar gwamnatin da za ta gaje shi ta san da su. Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa Kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu  cewa ya yi maganar makaman Amosun ba wata badakala ba ce.

Karuwar shigar makamai a hannun farar hula dai yana daya daga cikin dalilan da suka ta’azzara lalacewar tsaro na ayyukan ta’addanci, fashi da makami da fadace-fadacen kabilanci da kuma na addini a Najeriya. Wadannan tashin-tashina da suke faruwa suna kuma cin rayukan dubban jama’a tare da kawo asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira. Haka nan shigar makaman hannun farar hula ana alakanta shi da zama musabbabin fadan makiyaya da manoma da kuma matsalar garkuwa da mutane. Mallakar makamai ba bisa ka’ida ba laifi ne a karkashin dokar mallakar makamai ta 1984 da kuma ta 1990 na dokokin Najeriya.

Koma dai yaya abin yake a kan wannan badakala, muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi kyakkyawan bincike a kan wannan lamari na mika makamai da tsohon Gwamna Amosun ya yi. Ya kamata binciken ya gano shin ko Amosun ya samu lasisin mallakar makaman daga Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro ko kuma a’a? In kuma ba haka ba ya kamata a gano shin yaya aka yi jami’’an Kwastam ba su iya gano wadannan makamai ba a lokacin da aka shigo da su? Haka kuma nauyi ne akan masu binciken su gano cewa in ma har an ba shi lasisin , shin yawan makaman da aka ba shi damar sayen ne ya mika ga jami’an tsaron ko kuwa? Domin akwai yiyuwar tuntuni wasu makaman sun fada hannun batagari. Sannan sakamakon binciken tilas ne a bayyana wa duniya shi don a ilimantar da jama’a shin ko Amosun din a matsayinsa na Gwamna ya cika sharuddan lasisi kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar.