✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rumfar kamfe din Buhari ta rufta ta kashe mutum daya a Maiduguri

Cinkoson magoya bayan Jam’iyyar APC da suka yi dafifi a filin wasa na Ramat da ke garin Maiduguri, don gane wa idanunsu yadda yakin neman…

Cinkoson magoya bayan Jam’iyyar APC da suka yi dafifi a filin wasa na Ramat da ke garin Maiduguri, don gane wa idanunsu yadda yakin neman zaben Shugaba Buhari yake gudana a ranar Litinin da ya gabata, ya haifar da rushewar daya daga cikin manyan rumfunan da mutane suka taru.

Babbar rumfar ta rushe ne bayan nauyin mutanen kuma ta rufto bisa kan mutanen da suke karkashint, inda ta yi sanadiyar rasuwar mutun daya tare da jikkata sama da 40. Nan da nan jami’an agaji suka garzaya da mutanen zuwa Asibitin Kwararru da ke garin Maiduguri, inda kuma tuni Shugaba Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya faru da su.

Shugaba Buhari ya nanata kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arzikin kasa da inganta harkar tsaro da kuma na noma, inda ya yi bayanin cewa in har ya samu nasara a zaben zai ci gaba ne daga inda ya tsaya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Usman Mamman Durkwa ya ziyarci mutanen da suka jikkata a ruftowar rumfar, ya kuma yi fatan Allah Ya ba su lafiya.