✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar Sojin Aljeriya ta bukaci a cire Shugaba Bouteflika

Shugaban Rundunar Sojojin Aljeriya ya bukaci a ayyana Shugaban Kasar Abdelaziz Bouteflika a matsayin mara lafiya, wanda ba zai iya jan ragamar mulkin kasar ba.…

Shugaban Rundunar Sojojin Aljeriya ya bukaci a ayyana Shugaban Kasar Abdelaziz Bouteflika a matsayin mara lafiya, wanda ba zai iya jan ragamar mulkin kasar ba.

Da yake magana ta gidan talabijin din kasar Laftanal Janar Ahmed Gaed Salah ya ce: “Ya zama dole mu gaggauta nemo bakin zaren rikicin nan ta hanyar doka.”

Laftanal Janar  Gaed Salah din ya bukaci a yi amfani da sashe na 102 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bayar da dama a ayyana Shugaban Kasa da mara lafiya, ko ba zai iya mulki ba.

Tun a baya dai shugaban ya bayyana cewa ba zai yi takara ba a karo na biyar a zaben da ke tafe wanda aka jinkirta.

Sai dai duk da haka wadansu mutanen kasar sun ci gaba da zanga-zanga tare da zargin shugaban mai shekara 82 da yunkurin tsawaita wa’adin mulkinsa.

Tsoma bakin da shugaban sojojin ya yi shi ne ci gaba na baya-bayan nan da aka samu bayan makonnin da aka shafe ana zanga-zanga a kasar.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito lokacin da Shugaban Kasar ya yi yunkurin ci gaba da mulki karo na biyar duk da cewa yana fama da rashin lafiyar da har magana ke yi masa wahala, kuma ya kasance yana zaune ne a kujerar guragu. Amma daga baya da matsi ya yi yawa, sai ya hakura da zarcewa, amma aka jinkirta zaben.