✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rungumar aikin fadama ne ya dace da Najeriya – Sarkin Dutse

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dokta Nuhu Muhammad Sunusi ya nuna farin cikinsa game da yadda matasa suka rungumi harkar noman fadama a Jihar Jigawa da…

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dokta Nuhu Muhammad Sunusi ya nuna farin cikinsa game da yadda matasa suka rungumi harkar noman fadama a Jihar Jigawa da nufin taimakawa Gwamnatin Tarayya kan aniyarta da kuma farfado da kamfanonin kasar nan da suka dukurshe

Mai Martaba Sarkin ya fadi haka ne a daidai lokacin da shugabannin manoman fadama na kasa suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a cikin wannan mako a karkashin jagorancin shugaban kungiyar fadama ta 3 Mista Oyinbanji.

Sarkin ya ce sauya akalar Najeriya zuwa aikin gona abu ne da ya dace domin hakan ya fara dora kasar nan akan sikeli na daidai kamar yadda ta taso tun asali, sai kuma ya nuna takaicinsa game da yadda shugabannin baya suka yi watsi da harkokin aikin gona saboda gazawar wasu mutane marasa kishin kasa.

Sarkin ya ce babu kasar da take iya dogaro da kanta wajen ciyar da kasa dole sai jama’ar kasar sun rungumi harkokin noma hannu biyu kamar yadda gwamnatin Najeriya ta bullo da shi, an sha yin kurin haka amma shirin baya dorewa a Najeriya saboda wasu daga cikin ma’aikatan gwamnati suke wa shirin zagon kasa.

Sabanin sauran kasashen duniya wadanda suka fara irin wannan shiri yanzu kasashensu sun ci gaba sosai sabanin Najeriya, sannan ya shawarci jami’o’in kasar nan da su bude kwasa-kwasai da zasu taimaka wajen fadakar da manoma da makiyaya a tsangayar karatunsu, ta yin haka ne za a iya samun raguwar rigingimun manoma da makiyaya a fadin kasar nan. Sarkin ya ce ba komai ne yake haddasa rikicin ba illa karancin ilimi.

Shi ma da yake maida jawabi, babban jami’in shirin na fadama a jahar Jigawa, Malam Aminu Isah Ringim ya ce an zabi kananan hukumomi 23 a jihar nan, wadanda ake yin noman fadamar a kokarin gwamnati na samawa matasa aikin yi tare da farfado da aikin noma da kuma cika burin gwamnatin tarayya na dawo da aiki a masana’antun kasar nan.

Ringim ya kara da da cewar kimanin hekta dubu 10 da 380 aka rabawa matasan da aka zabo daga kananan hukumomi 23 na jahar ta hanyar sanya matasan su kafa kungiyoyin manoma na fadama a daukacin kananan hukumomin da aka zaba kuma aka samar masu da rijiyoyin da suke amfani da su wajen aikin gonar.

Ringim ya shawarci matasan da suka amfana da tallafin aikin noman na fadama a jahar Jigawa da su yi amfani da su domin shekara mai zuwa ba sune za a baiwa tallafin ba, za a sake bawa wadanda ba su amfana ba ne domin ganin shirin ya shafi kowa kai tsaye.

Shi kuwa shugaban ma’aikatan jihar ta Jigawa, Alhaji Inuwa Tahir a lokacin da ya amshi bakuncin shugabannin kungiyar ta fadama a ofishinsa kasancewar shi ne ya wakilci gwamnan jihar ta Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar yabawa ya yi da kokarin kungiyar manoman ta fadama game da yadda take tallafawa manoma a fadin kasar nan da kuma yadda shirin noman fadama ya samu karbuwa a fadin Najeriya.