✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ya kamata ku sani kan rushe SARS

Abubuwan da ya kamata ku sani game da rushe sashen ’yan sanda na SARS mai yaki da fashi a Najeriya

Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani bayan soke ayyukan sashen ’yan sanda masu yaki da fashi (SARS) a Najeriya:

  • Ranar Lahadi 11 ga Oktoba, 2020, Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya soke SARS a fadin kasar.
  • Za a sauya wa dukkannin jami’an da ke aiki karkashin sashen wurin aiki a rundunar.
  • Nan gaba za a bullo da sabon tsarin yakar fashi da sauran manyan laifuka.
  • Za a bude zauren tattaunawar ’yan kasa da masu ruwa da hukumomin ’yan sanda akai-akai game matsalolin al’umma.
  • Domin tabbatar da hukunta jami’an da ke zaluntar mutane za a kafa tawagar bincike da zai kunshi kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Idan ba a manta ba, rushe sashen wanda daga baya ake kira FSARS na zuwa ne bayan kwanaki da aka shafe ana zanga-zangar neman hakan a sassan Najeriya bisa zargin jami’anta da cin zalin jama’a.

Shugabbani da mafutika da matasa sun yi ta Allahwadai da yadda jami’an ke zaluntar jama’a, lamarin da ya sa Shugaban Kasa cewa zai gyara wa rundunar zama.

Buhari ya kuma umarci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da ya kama tare da hukunta jami’an da zargi ya tabbata a kansu domin yin maganin ’yan sandan da ke daukar doka a hannunsu.

Ko da yake wasu ’yan Najeriya na ganin gyaran fuska ya kamata a yi wa rundunar, wasu na ganin hakan ba zai biya bukata ba domin a baya ma an yi irin wadannan koke-koke a kan jami’an, wanda sakamakonsa ne aka sauya wa rundunar suna daga SARS.

Akwai kuma masu ganin cewa sokewar ba za ta kawo wani sauyi ba domin jami’an da ake zargin za su ci gaba da aikin dan sanda a kasar da ake yawan zargin jami’an ’yan sanda da karbar na goro da kuma amfani da kakinsu wajen danne hakkin jama’a.

Don haka suke ganin abin da ya fi dacewa shi ne wayar da kan jami’an ’yan sanda ta yadda za su fahimci muhimmancin aikinsu da kuma gudanar da shi cikin kare hakkin jama’a.