Da Dumi Dumi

Ruwa ya ci yaro a kogi

Ruwa ya ci wani yaro mai suna Christian, wanda dalibi ne a makarantar firamarer  Ibesikpo, a Layin Ambo da ke Kalaba a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu. Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa, an aiki yara ne dibar ruwa a kogin ne sai ya bi su shi ma da nasa abin dibar ruwan, kuma da ya je sai ya iske yaran sun shiga ruwan suna ninkaya shi kuma bai san yadda ake yi ba, sai ya fada da nufin ya  yi ninkayar kamar yadda ya ga yara abokansa suna yi daga nan ya kasa, sai ruwa ya cika masa baki da hanci ya nutse.

Makwabcin iyayen yaron,  mai suna Ibanga Peter, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Ba a san ruwa ya ci yaron ba, sai bayan da aka jima bai dawo daga wurin diban ruwan ba, inda aka bi sawunsa sai aka ga gawarsa tana yawo a saman ruwa.”

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin iyayen yaron amma ba sa  gari, sai dai an tababtar da cewa mahaifin yaron ya ce kada a binne shi sai ya dawo daga Jihar Edo.

Kakakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin.

 

ADVERTISEMENT

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya