✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan rafi ya ci budurwa a Kaduna

Ranar Lahadin nan ne wata badurwa ta rasa ranta a sakamakon nutsewa cikin ruwa da ta yi a lokacin da matukin babur mai taya uku…

Ranar Lahadin nan ne wata badurwa ta rasa ranta a sakamakon nutsewa cikin ruwa da ta yi a lokacin da matukin babur mai taya uku wanda aka fi sani da suna Keke-Napep da take ciki ya yi kokarin tsallake gadar Hayin Malam Bello da ke a Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 6 na yamma a lokacin da ruwan rafin ya hau kan gadar unguwar a sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi a wannan rana.

Wasu daga cikin shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‎jama’a da yawa ne suka tsaya a bakin titin ganin cewa ruwan ya haura kan gadar amma shi matukin NAPEP din sai ya yi kokari wucewa ta cikin ruwan wanda hakan ya sa keken ta kife da su.

A cewar wani mai shago kusa da wurin da abin ya faru ya ce, wasu matasa ne suka yi kukan kura suka shiga cikin ruwan har Allah Ya sa suka ceto sauran mutum biyu da ke cikin keken inda ita kuma marigayiyar ruwa ya tafi da ita.

‎” Ta na cikin KEKE NAPEP ne lokacin da shi matukin ya yi kokarin bi ta cikin ruwan har ta kai ga kifewarsu amma matasa da ke kusa sun yi kokari har suka ceto mutanen da ke ciki amma ita ba’a ganta ba,” in ji shi.

Shi dai wannan gada na Hayin Malam Bello a duk shekara idan aka yi ruwan sama mai yawa ruwa kan shanye gadar na tsawon wasu mintuna wanda hakan ke hana mutune wucewa.