ADVERTISEMENT

Ruwan sama ya yi gyara a Jihar Jigawa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya raba mazauna Unguwar Bakwato da Fagoji da Maranjuwa da Kasarau da Unguwar Zai da kuma Yalwawa da gidajensu.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe hudu da rabi na yamma sakamakon ruwan da aka tafka kamar da bakin kwarya.

ADVERTISEMENT

Saboda karfin ruwan saman, masu ababen hawa sai da suka tsaya a gefen hanya don gudun kada wani abu ya same su idan suna tafiya.

A gefe daya lambatun da ke makare da bola duk sun yi ambaliya inda suka cika tituna da shara al’amarin da ake ganin ya faru ne saboda rashin tsaftace lambatun kafin saukar ruwan.

ADVERTISEMENT

Sai dai binciken Aminiya ya nuna da yawa daga cikin mazauna unguwannin da abin ya shafa suna da halayyar zuba shara ne a cikin lambatun kafin saukar ruwan sama.

Bayan aukuwar lamarin, mutane da dama sun yi gudun hijira ne zuwa gidajen makwfta don samun mafaka.

Wani wanda gidansa ya rushe a Unguwar Bakwato Malam Ibrahim Fagoji ya nuna alhininsa game da faruwar lamarin inda ya roki gwamnati musamman ta Jiha da ta karamar hukuma da ta kai musu dauki.

Ya ce da yawa daga cikinsu wanda abin ya shafa talakawa ne musamman a wannan lokaci da ake cikin matsalar rashin kudi.

Sauran mutanen da abin ya shafa a zantawarsu da wakilinmu sun tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun nemi taimakon gaggawa daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da kuma gwamnatin jiha da ta karamar hukuma.