✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sa Ubangiji da farko (2)

“Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinSa, har ma za a ƙara muku dukkan waɗannan abubuwa.” –…

Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinSa, har ma za a ƙara muku dukkan waɗannan abubuwa.” – Matiyu 6:33

Barkanmu da sake saduwa a wannan mako. Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa da alheranSa zuwa gare mu. Za mu ci gaba da nazarinmu a kan sa Ubangiji da farko cikin komai. Kamar yadda muka karanta abin da ya fi muhimmanci a rayuwar dan Adam shi ne Ubangiji Mahalicinsa, domin Shi ne farko da kuma karshen komai da kowa, Shi kadai Ya san abin da zai faru yanzu da nan gaba da kuma har abada cikin rayuwar dan Adam. Da sanin haka sai mu sa zuci mu girmama Ubangiji Allah a koyaushe cikin rayuwarmu da farko domin mu ci moriyar albarkarSa. Akwai abubuwa da dama da ba mu da sanin cewa suna da albarka sai idan mun sa Ubangiji da farko cikin rayuwarmu da harkokinmu na yau da kullum. Misali, za ka ga wani dan kasuwa ko ma’aikaci da ke da kwazo cikin harkokinsa amma ba ya da kwanciyar hankali, musamman lokacin da harkokin ba su tafiya yadda ya zata ko ya shirya wa kansa, wani lokaci har wadansu kan sa kansu cikin halin rashin lafiya, hauka ko kisan kai, me ke kawo irin wannan yanayi? Rashin sanin Ubangiji da kuma albarkar da ke cikin sa Shi da farko cikin komai. Domin danka komai cikin hannun Ubangiji da farko kan ba da kariya, riba da albarka. (Karin Magana 16:3) “Ka roƙi Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.  Ka roki Ubangiji kan harkokinka na yau? Gama mun ji, mun gani, mun kuma shaida abubuwan da Ubangiji ke yi cikin rayuwar mai bi na gaskiya. Rashin sa Ubangiji cikin harkoki da rayuwar dan Adam alama ce da ke nuna kaunar da muke da ita ga kayan duniya ta wurin ikon kanmu, hatta nuna kauna ga dan uwanka ma zai yi wuya. Yesu Almasihu ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan ƙarfinka da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan uwanka kamar kanka.” (Luka 10:27).  Mu sani fa cewa idan Ubangiji ba Ya cikin harkokinmu na yau da kullum babu shakka mun gayyaci Shaidan ke nan. Shi ya sa za ka ga mutane da dama na fama da rashin lafiya (domin kwadayin kayan duniya), wadansu ma na tunanin kisan kai (da talaka da mai dukiya) da sauransu. Wadannan halaye kuwa ba daga wurin Ubangiji ba ne domin Ubangiji ba zai taba sa ka yi kisan kai ba, ba zai kuma sa ka kwadayin kayan duniya ba, domin irin wadannan halaye sun saba wa maganarSa, gama maganar Sa na cewa, “Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha’awa irin na halin mutuntaka, da sha’awar ido da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ce. Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” (1 Yahaya 2:15-17). Abin da Ubangiji ke bukata a gare mu shi ne, mu kaunace Shi da dukan ranmu, (Kolosiyawa 3:1-4), “To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah. Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.” Haka kuma kaunarSa kuwa sai mu bide Shi da farko cikin kowane irin hali. Idan kuma rashin biyan bukata ne ke hana ka bidar Ubangiji da farko cikin harkokinka da rayuwarka, ka ji abin da maganar Allah ke fadi cikin Littafin Matiyu 6:31-33: “Don haka kada ku damu, cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuwa, ‘Me za mu sa?’ Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa Ya san kuna bukatarsu duka. Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukkan waɗannan abubuwa.” To, idan har Ubangiji na sane da bukatunmu, me zai hana mu neman fuskarSa da farko cikin rayuwarmu? Mu fito daga cikin halin rashin sani, mu nemi fuskar Ubangiji tun yana samuwa domin mu mori albarkar da ke kunshe cikin zumunci da Shi.

Sai mu zama da sanin cewa “Ai, daga gare Shi ne, ta wurinSa kuma, dukkan abubuwa suke, Shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka ta tabbata a gare Shi har abada. Amin” (Romawa 6:36).

Bari mu sa Ubangiji Allah da farko cikin komai a wannan lokaci, mu sabunta rayuwarmu, mu nemi nufinSa cikin komai a koyaushe, mu zama masu binciken LittafinSa Mai tsarki, masu addu’a kuma a koyaushe kamar yadda Ya umarce mu mu yi, ta wurin yin haka ne za mu yi kusa da Shi, Shi kuma tare da mu.