Search
Subscribe
Sababbin fuskoki a ministocin Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Sababbin fuskoki a ministocin Buhari

A shekaranjiya Laraba ce Majalisar Dattawa ta soma tantance sunayen ministocin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika musu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta takardar da ke dauke da jerin sunayen mutanen da za a nada ministocin a zauran majalisa, bayan wani taron sirri da suka gudanar a ranar Talata da ta gabata.

“An soma tantance sunayen ministocin ne dai shekaranjiya Laraba. Dukkan aikace-aikacen majalisar an dage shi har sai an kammala tantance sunayen da Shugaban Kasa ya aiko da su domin a sahale masa ya nada ’yan majalisar zartarwarsa,” inji Lawan.

Tsarin Mulkin Najeriya ne ya sahale wa Shugaban Kasa ya zabi ministocin da zai yi aiki da su, sannan ya aika wa Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma sahalewa, kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulkin 1999, sashi na 147 (2) ya tanada, kamar yadda yake kunshe cikin wasikar da Shugaban Kasar ya aike wa majalisar a ranar Litinin da ta gabata.

Aminiya ta samu bayanin cewa sunayen da Shugaban Kasar ya aike ga majalisar sun zarta yawan sunayen da ya aike da su a farkon zangon mulkinsa a shekarar 2015, inda ministoci 36 Shugaban ya nada kawai a wancan lokacin. Shugaban dai ya sha alwashin kara yawan ministocin da zai nada a wannan karo.

Jihohin Anambara da Bauchi da Edo da Kaduna da Kano da Kwara da kuma Legas, duk sun rabauta da kujeru biyu kowace. A yayin da Jihar Kaduna a Shiyyar Arewa maso Yamma kadai ce ta rabauta da kujeru biyu, idan aka hada ta da sauran takwarorinta.

Shugaba Buhari ya kara yawan mata a cikin ministocin nasa da kujera daya, inda suka zama bakwai, sabanin mata shida da ya nada a matsayin ministoci a wa’adin farko. Sannan ya kara yawan ’yan Majalisar Zartarwar tasa daga 36 a shekarar 2015 zuwa 43 a wa’adinsa na karshe.

A farkon wa’adin mulkin Shugaban Kasar, ya nada Amina Mohammed daga Gombe da Zainab Ahmed daga Kaduna da Kemi Adeosun daga Ogun da A’isha Abubakar daga Sakkwato da A’isha Alhassan daga Taraba da kuma Khadija Bukar Abba daga Yobe.

Daga cikin ministoci mata, A’isha Abubakar da Zainab Ahmed ne suka kai karshen zangonsa na farko, yayin da ragowar hudun suka fice daga gwamnatin a kan wasu dalilai daban-daban.

Akwai kimanin tsofaffin gwamnoni 8 da suka shigo cikin jerin mutanen da ake tantancewa da kuma sanatoci bakwai. Bisa al’ada duk wani tsohon dan majalisa zai je ya yi gaisuwa ne kawai a gaban ’yan majalisar, ba tare da sun yi masa wasu tambayoyi ba.

Ga takaitaccen tarihin wadansu daga cikin sababbin ministocin:

Sunday Dare, Jihar Oyo: Shi ne wanda Shugaba Buhari ya tura sunansa a matsayin Minista daga Jihar Uyo. Sunday Dare dan asalin Ogbomoso ta Arewa kafin a mika sunansa, Kwamishina ne Mai kula da Sashen Masu Ruwa- da-Tsaki a Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).

Ya taba zama Shugaban Ma’aikata kuma Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Sadarwa ga Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi digirinsa na farko a Harkokin Kasashen Waje (International Studies) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya yi digiri na biyu a fannin Shari’a a Jami’ar Jos. Ya kuma yi kwas kan aikin jarida a Jami’ar Harbard. Sannan ya yi aiki kwantaragi a Jami’ar New York da ke Amurka.

Ya shugabanci Sashen Hausa na Muryar Amurka da ke Washington DC daga shekarar 2001 zuwa 2009. Yana daga cikin wadanda suka assasa mujallar The News da ta Tempo a lokacin mulkin soja.

Festus Keyamo, Jihar Delta: An haifi Festus Keyamo a ranar 21 ga Janairun 1970 a garin Ughelli da ke Jihar Delta. Babban Lauya ne kuma marubuci da ya dade yana fafutikar kare hakkin dan Adam. Ya yi digirinsa a fannin Shari’a a Jami’ar Ambrose Alli da ke Jihar Edo. Sannan ya zama kwararren lauya a Disamban 1993.

Shi ne ya kasance mai magana da yawun kwamitin yakin sake zaben Shugaba Buhari a bana.

Isa Ali Pantami, Jihar Gombe: An haifi Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktoban 1972 a Gombe. Ya fara karatun addini kafin ya shiga makarantar boko a Pantami da ke Jihar Gombe. Sannan rahotanni sun nuna cewa bayan ya kammala sakandare sai da ya sake yin shekara biyu yana karatun addini kafin ya shiga jami’a.

Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi a shekarar 2003, inda ya karanci fasahar kwamfuta. Ya yi digiri na biyu a shekarar 2003 da kuma digiri na uku a Jami’ar Robert Gordon da ke Aberdeen, a kasar Scotland.

Ya halarci kwas a kasashen Amurka da Switzerland da sauransu. Ya kuma yi aikin koyarwa a Jami’ar ATBU da Jami’ar Madina, kafin daga bisani a ba shi Shugabancin Hukumar Kula da Fashar Sadawar  Zamani ta Najeriya (NITDA).

Sadiya Umar Farouk, Jihar Zamfara: Sadiya ’yar asalin Karamar Hukumar Zurmi ce daga Jihar Zamfara. Ta fara karatunta a Kwalejin ’Yan Mata ta Tarayya da ke Gusau, kana ta yi digirinta na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Al’amuran Mulki, wanda ta kammala a 1998 kafin ta sake komawa jami’ar ta yi digirinta na biyu.

Ta fara aiki lokacin da ta je yi wa kasa hidima a Majalisar Dokoki ta Kasa, inda bayan kammala hidimar kasa ta fara aiki da Kamfanin Sufuri na Pinnacle tsakanin shekarar 2001 zuwa 2003, kafin ta samu aiki da Majalisar Dokokin a matsayin jami’ar gudanarwa, inda daga bisani ta ajiye aiki ta shiga harkokin siyasa. Ta rike mukamin Ma’ajin Kudi ta Kasa ta Jami’yyar CPC, sannan ta rike wannan matsayi a karkashin Jami’yyar APC, a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014. An nada Sadiya a matsayin Babbar Kwamishiniya Mai Kula da ’Yan Gudun Hijira, mukamin da take rike da shi har ta samu zama Minista a wannan lokaci.

Ramatu Tijjani, Jihar Kogi: Ta kasance ’yar gidan sarauta daga iyalan marigayi Alhaji Sidi Ali Mamman Bawan Allah na Lakwaja a Jihar Kogi. Ta fara karatunta a makarantar firamare ta Dawaki a garin Suleja a 1976. Bayan ta kammala ne ta samu shiga Kwalejin ’Yan Mata ta Tarayya da ke Minna a Jihar Neja, inda ta samu damar shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ta yi digirinta na farko a kan tsara birane. Ta yi aikin yi wa kasa hidima a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya. Ta yi digirinta na biyu daga Jami’ar Jihar Nassarawa da ke Keffi.

Ta shiga cikin harkokin siyasa bayan ta yi ayyuka da dama a fannoni daban-daban, inda ta fara zama Mai bai wa Shugaban Karamar Hukumar Gwagwalada Shawara a kan Al’amuran Mata da Matasa. Ta kuma zama Mataimakiyar Shugaban Jami’yyar ANPP na Shiyyar Arewa ta Tsakiya. Ta zamo Shugabar Mata ta wannan jam’iyyar, har ta kai ta ci gaba da rike wannan mukami a Jam’iyyar APC. Tana rike da wannan mukami ne aka zabo ta domin ta zama Minista.

Gbemisola Rukayyah Saraki: Fittaciyar ’yar siyasa ce daga Jihar Kwara. Ta taba zama ’yar Majalisar Wakilai ta Tarayya, inda ta wakilci mazabar Asa da Ilori ta Yamma, kafin a shekarar 2003 a zabe ta a matsayin Sanata a karkashin Jam’iyyar PDP inda ta wakilci Kwara ta Tsakiya. Ta canja sheka zuwa Jam’iyyar APC watanni kadan kafin a gudanar da zaben Shugaban Kasa.

Ta halarci Jami’ar Sussed da ke kasar Amurka, inda ta yi digirinta na farko a fannin tattalin arziki. Ta yi aikin yi wa kasa hidima a Bankin Kasuwanci da Raya Masana’antu, ta fara aiki a rusasshen bankin nan na Societe General Bank a matsayin shugabar sashin kula da hada-hadar kudade. Ta kuma zama Babbar Darakta a Kamfanin Inshora na Ashmount da ke Legas.

Maryam Yalwaji Katagum, Jihar Bauchi: An haifi Maryam Katagum ne a ranar 18 ga Nuwamban 1954 a Azare da ke Jihar Bauchi. Ta yi karatu a Najeriya da Ingila, inda take da digiri  a Igilishi da takardar shaida kan Ilimi daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Tana da digiri na biyu kan Shugabanci da Tsare-Tsare daga Jami’ar Legas da kuma satifike nak Tsara Ci gaba da Tsara Ayyuka a Aikace daga Jami’ar Unibersity College da ke Landan. Ta yi hidimar kasa a Hukumar Ruwa ta Filato, kuma ta yi aiki a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Azare da Hukumar Sikolaship ta Kasa a Legas kafin a tura ta Hukumar UNIESCO a matsayin wakiliyar Najeriya.

Ta rike mukamai da dama a Hukumar UNESCO, inda mukami na karshe da take rike da shi shi ne na Jakadiya kuma Babbar Wakiliyar Najeriya a UNESCO tun daga Yunin shekarar 2009.

Bashir Salihi Magashi (Kano): Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya) ya taba zama Gwamnan Jihar Sakkwato daga Agustan 1990 zuwa Janairun 1992 lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida. Magashi yana da digiri a aikin lauya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya kuma samu lambar karramawa ta kasa ta CFR.

Ya taba zama Kwamandan Brigade of Guards a 1993 yana daya daga cikin na hannun damar Janar Babangida da Janar Abacha. A shekarar 2002, an nada shi Mai Bayar da Shawara kan Shari’a na Jam’iyyar ANPP, kuma a  shekarar 2007, ya yi takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar DPP.

Sharon Ikeazor (Anambra): Sharon Ikeazor, ita ce Shugabar Hukumar Kula da Fansho ta PTAD da Shugaba Buhari ya nada ranar 26 ga Satumban 2016.

A shekararta ta farko ta gabatar da tsare-tsare da dama da suka kawo sauyi a Hukumar PTAD.

Sharon tana da digiri a fannin shari’a daga Jami’ar Benin da kuma takardar shaidar kammala makarantar koyon shari’a a 1985.

A shekarar  2011, ta zama shugabar mata ta Jam’iyyar CPC.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin