Da Dumi Dumi

Saboda hana satar jarrabawa malami ya umarci dalibai su sanya katan a kansu

Wani malami a kasar Meziko ya umarci daliban wata kwaleji su sanya katan din kwali a kansu don rufe duk wata hanya da za ta iya sanya wani dalibi hangen amsar dan uwansa a matsayin dabarar hana satar jarrabawa.

Malamin wanda ke aiki a Kwalejin Campus 01 na College of Bachelors da ke garin El Sabinal, babban birnin Tladcala a Jihar Medican, mai suna Luis Juarez Tedis, an tuhume shi da tauye hakkin dan Adam kan umarnin da ya bai wa daliban lokacin da suke rubuta jarrabawar bayan da aka fitar hoton lokacin da yake binciken masu jarrabawar sanye da katan din.

Iyayen daliban sun yi ta yada hotunan ’ya’yansu a shafukan sada zumunta na zamani lokacin da aka tsare yaran suna rubuta jarrabawar a kwalejin. Kuma sun bukaci hukumomin ilimi na Meziko su kori malamin da ya umarci daliban da aikata haka lokacin da suke jarrabawa.

A cikin korafin da iyayen daliban suka wallafa akwai mai cewa, “Mun yi Allah wadai da cin mutuncin daliban da malamin ya yi a  Kwalejin Campus 01 na El Sabinal, Tladcala. Tare da fallasa yadda abin da Luis Juarez Tedis, ke yi wa daliban kwalejin.” Iyayen sun ce, sun bai wa ’ya’yansu tarbiyya bai kamata a rika tauye hakkin manyan gobe ba, don haka a gaggauta korar malamin. Muna fata hukumomin da suke da hakki za su dauki kwararan matakai wajen dakatar da malamin, wannan sam bai dace ba a muhallin koyar da ilimi…” Kamar yadda wasu iyayen suka wallafa a shafin Facebook.

Hoton katan din da daliban suka saka a kansu suna da kofar ganin abin da suke rubutawa, ta hanyar da ba za su iya yin waiwaye ko juya wuyansu ba.

ADVERTISEMENT

Dubban mabiya shafukan sada zumunta sun yi ta yada hotunan tare da sukar malamin da ya umarci daliban. Sai dai a wani bangaren wadansu sun bayyana ra’ayinsu cewa, abin da malamin ya yi wa daliban zai iya dakile satar jarrabawa a makarantu don haka suke jinjina masa.

A cikin masu sharhi game da hotunan daliban, wani ya ce “Malamin ya aikata aiki mai kyau da ba zai cutar da daliban ba, wannan ba abin da iyaye za su damu da shi ba ne, wannan babban abu ne na kare su daga satar jarrabawa.” Don haka suke goyon bayan abin da malamin ya yi wa daliban.

Da manema labarai suka tambayi wani da ya halarci zauren jarrabawar Mista Juarez Tedis,  ya ce, an umarci daliban ne kawai su rufe kansu da katan don kauce wa satar jarrabawa.

Share