✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saboda rashin haihuwa miji ya cinna wa matarsa wuta

Wani magidanci ya cinna wa matarsa wuta a gundumar Rod El Farag da ke Alkahira babban birnin Masar saboda rashin haihuwarta a tsawon shekara uku…

Wani magidanci ya cinna wa matarsa wuta a gundumar Rod El Farag da ke Alkahira babban birnin Masar saboda rashin haihuwarta a tsawon shekara uku da aurensu.

Jaridar kasar da ake wallafawa kullum mai suna Al-Wafd, ta ce magidancin mai suna Mohammed ya daure matarsa mai suna Aya, sannan ya cinna mata wuta, ya barta tana c a kusa da bangon dakin gidan iyayensa inda suke zaune, sannan ya ki kiran jami’an bayar da agajin gaggawa.

Bayan makwabtan gidan sun kira ’yan sandan da jami’an kiwon lafiya sun tarar da matar kusan kashi 70 cikin 100 na jikinta ya kuna, sannan daya daga cikin huhunta ya samu matsala saboda kunar wutar, ba ta samu ta kubce daga babbaka ta da mijin ya yi niyyar yi ba.

Makwabtan gidan su Aya, sun ce mahaifiyar Mohammed da shi Mohammed din sun dade suna kyararta saboda rashin haihuwar, inda suke ganin ita ba mai haihuwa ba ce. A yanzu haka hukuma na tsare da Mohammed ana ci gaba tuhumarsa.

A kasar Masar kimanin mata miliyan 1.5 ne suke fuskantar tsangwama da matsalolin zaman aure duk shekara, yayin da ake samun matan da ke fuskantar irin wannan matsalar akalla dubu 4 duk rana.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, matan aure daga shekara 15 zuwa 49 aka bayyana cewa, suke fuskantar irin wannan kalubale duk da yake rahoton ya ce akwai irin wadannan matsalolin da ba a bayyana ba.

Dokar kasar Masar ta ce, mata na bukatar a kare hakkinsu musamman a gidajen aurensu, wulakanta su babban laifi ne.

A shekarar 2017 Majalisar Zartarwar Mata ta Kasar  (NCW) ta kaddamar da dokar da ta yanke hukuncin irin wannan laifi ciki har da daurin shekara daya a gidan yari ga mazan da suka wulakanta matansu.