✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon rikici ya haddasa rasa rayuka a Jihar Taraba

Wani sabon fada wanda ke da alaka da addini da kabilanci ya sake barkewa a garin Gindin dorawa da ke karamar Hukumar Wukari, Jihar Taraba.…

Wani sabon fada wanda ke da alaka da addini da kabilanci ya sake barkewa a garin Gindin dorawa da ke karamar Hukumar Wukari, Jihar Taraba.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, fadan wanda aka fara da safiyar Larabar da ta gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawan gaske.
Majiyar ta bayyana cewa matasan Jukunawa ne dauke da bindigogi da saura miyagun makamai suka auka wa al’ummar Hausa-Fulani a lokacin da suke Sallar Asuba.
Majiyar ta kara da cewa, wannan lamari ya tilasta wa al’ummar Hausa-Fulani mayar da martani, wanda haka din ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawan gaske.
Wani mazaunin garin ta bangaren Hausa-Fulani, mai suna Malam Haruna Hamidu ya ce su ba su san hawa ba, ba su san sauka ba sai suka sami kansu a cikin farmaki daga ’yan kabilar Jukunawa.
Ya ce dama ’yan kabilar Jukunawa sun saba kai wa al’ummar Hausa-Fulani farmaki, inda suke kashe al’ummarsu tare da kona dukiyarsu.
Ya ce ganin cewa hukuma ba ta daukar wani mataki kan al’ummar Jukun, shi ya sa suke cin karensu ba babbaka.
A wannan sabon fadan an kona fiye da rabin garin tare da kona ababen hawa tare da hatsi, lamarin da ya tilasta wa jama’ar yankin kaurace wa gidajensu.
Yankin na Wukari ya fuskanci rikice-rikice tsakanin ’yan kabilar Jukun da al’ummar Hausawa da Fulani.
’Yan kabilar Jukun ta bakin wani mai suna Mista John Bulus, ya ce su ba su da hannu a cikin wannan lamari na baya-bayan nan. Ya ce akwai bukatar jama’ar yankin su hada hannu wajen maido da zaman lafiya a yankin, wanda fadace-fadace ya lalata.
Wata majiya mai tushe daga yanki ta shida wa wakilinmu cewa kura ta lafa bayan da aka tura ’yan sanda da sojoji, don maido da doka da zaman lafiya kuma ma har masu motoci sun soma bin hanyar wuraren da fadan ya tilasta wa kauracewa.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa rikicin da ke faruwa a yankin na Wukari da Ibbi bai da alaka da addini, illa kawai ’yan siyasa ne kawai ke amfani da addini don cin ma burinsu.
Binciken kuma ya nuna cewa kusan kowane gida a yankin akwai munanan makamai, wadanda aka tanada don mugun nufi.
A halin da ake ciki kuma an maido da zaman lafiya a garin Dananacha da ke karamar Hukumar Gassol, bayan wata tarzoma da matasan garin suka gudanar, bayan gano gawar wani mutumin garin da aka yi kuma an yanke wasu sassa na jikinsa.
Ganin gawar wannan mutumin da aka yi, ta tunzura matasan garin, inda suka gudanar da zanga-zanga tare da kona tayoyi. Tura ’yan sandan kwantar da tarzoma zuwa garin cikin gaggawa, shi ne ya taimaka waje hana tarzomar rikidewa zuwa rikicin kabilance da na addini.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandar Jihar Taraba, ASP Joseph Kwaji da wakilinmu ya tuntube shi, ya tabbatar da faruwar wannan rikici. Ya ce tuni aka tura jami’an tsaro na soja da ’yan sanda, wadanda suka shawo kan al’amarin. Ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu komai ya lafa, al’umma sun ci gaba da gudanar da al’amuransu na rayuwa kamar yadda aka saba.