✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon salon dafa taliyar Indomie

Kamar yadda aka sani indomie taliya ce wadda ke da saukin nuna. Amma yadda wata za ta girka nata dabam yake da yadda wata matar…

Kamar yadda aka sani indomie taliya ce wadda ke da saukin nuna. Amma yadda wata za ta girka nata dabam yake da yadda wata matar za ta girka nata. Don haka ne a yau na kawo muku sabon salon girka indomie don a gwada a kuma tantance wanda ya fi dadi da kuma armashi. Kada a manta maigida yakan gaji da salon girki iri daya, shi ya sa nake so a mayar da hankali wajen koyon kowane irin salon girki.

Abubuwan da za a bukata:
· Indomie
·Attarugu
·Albasa
·Kifi banda
·Magi
·Man gyada
Hadi:
A dora ruwan zafi a wuta. Bayan ya tafasa sai a zuba taliyar indomie a ciki. idan ta tafasa, sai a sauke a wanke da ruwan dumi. A ajiye a gefe. Daga nan sai a yayyanka albasa da attarugu a kuma wanke kifi banda a cire kayar cikinta a ajiye.
A  sake dora tukunya a wuta a karo na biyu, sannan a zuba man gyada kadan  sannan a bi da yankakkiyar albasa da attarugu a yi ta juyawa har sai sun soyu sannan a zuba ruwa da kifi da magi daya sannan a rufe. Idan kifin ya nuna za a ji kanshi sai a dauko taliyar indomie a zuba sannan a gauraya. A dauko magin cikin taliyar indomin a barbada a sannan a gauraya. Sai a rufe don ruwan ya kone kafin a kwashe.
Shi ke nan girkin taliyar indomie ya yi, kuma uwargida za ta sanar da ni idan ta ji iyalai ciki har da maigida suna santi.