✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon salon tsaro muke yi a Jihar Oyo -Kwamishinan ’yan sanda

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammed Abdulkadir Indabawa ya bayyana cewa rundunarsa tana tsarin gudanar da sabon salon tsaro a jihar, wanda zai taimaka…

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo, Muhammed Abdulkadir Indabawa Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammed Abdulkadir Indabawa ya bayyana cewa rundunarsa tana tsarin gudanar da sabon salon tsaro a jihar, wanda zai taimaka wa samar da zaman lafiya da walwala fiye da na shekarun baya.
Kwamishinan, wanda ke fadin haka cikin hirarsu da wakilinmu, ya kara da cewa kodayake da ma suna gudanar da ayyukansu ta yadda ba sani ba sabo, a wannan sabon salon nasu za su kara jajircewa wajen ganin jama’ar jiha, mutanen kirki sun kara samun natsuwar gudanar da harkokinsu domin kuwa za su watsa aniyar’yan ta’adda masu tayar da zaune-tsaye.
Dangane da kamen da aka yi wa wadansu mutane kuwa, kwamishinan ya ce, “Kamen da jami’an tsaro suka yi wa wasu mutane 42 da ake zargin ’yan boko haram ne, an yi ne a jihohin Legas da Ogun  kawai, mu ba mu kama kowa a jihar Oyo ba. Kuma kamar yadda abokin aikina babban kwamandan rundunar soja ta 2 da ke Ibadan, Manjo Janar Ahmed Tijani Jibrin, ya yi bayani ga wata jarida kwanan baya cewa, dukkan jihohin da ke karkashin rundunar za su kasance cikin tsaro na musamman ne a dalilin rade radin cewa, ’yan boko haram suna shirin shigowa sashen Kudu maso Yamma, musamman Jihar Oyo, wannan ya sa mu daukar tsauraran matakan tsaro da za su taimaka mana wajen gano gaskiyar al’amarin ta yadda za mu yi maganinsa.” Kwamishina Indabawa ya ce, “Harkar tsaro ta kowa da kowa ce. Bai kamata ’yan Najeriya su rika dora alhakin tsaro ga ’yan sanda ko soja da SSS kadai ba. Babu yadda za mu ci gaba a Najeriya, sai idan mun nuna da kishin kasa a zukatanmu ta fannin hanzarta sanar da ’yan sanda bullar abubuwan da ba mu amince da su ba. A duk lokacin da mutane suka ga bawai, to, su hanzarta sanar da jami’an tsaro. Hakkinmu duka ne mu tabbatar da bayar da labarin bullar abubuwan da ba mu yarda da su ba ga jami’an tsaro, idan ka aikata haka, to ka zama cikakken dan kasa, mai kishin kasar haihuwarsa.”