Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sabon Sarkin Japan ya fara mulki bayan mahaifinsa ya yi murabus

Sabon sarkin Japan Naruhito
Sabon sarkin Japan Naruhito

Sabon Sarki Naruhito na Japan ya yi jawabinsa na fari bayan da ya dare karagar mulki, inda ya yi fatar samun farin ciki da zaman lafiya a duniya.

An gudanar da wani biki a Fadar Imperial shekaranjiya da ya dare karagar mulkin kasar.

ADVERTISEMENT

Wani sabon karni mai suna Reiwa – wanda ke nufin oda da tsari – ya fara ke nan har karshen mulkinsa.

Mahaifinsa Akihito mai shekara 85 ya kasance sarki na farko da ya sauka daga mulkinsa ranar Talata a tsawon fiye da shekara 200.

ADVERTISEMENT

Sarki Naruhito mai shekara 59 da haihuwa ya gode wa mahaifinsa tsohon Sarki Akihito.

“Ya gudanar da dukkan ayyukansa da sadaukar da kai na tsawon fiye da shekara 30,” inji shi. “Ya kuma nuna tausayawa ga gajiyayyun cikin al’ummarsa. Ina son mika godiya ta musamman da jinjina a gare shi.”

Sarki Akihito na kasar Japan ya kammala shirin sauka daga sarautar kasar domin dansa ya gaje shi.

Sarki Akihito na da shekara 85 da haihuwa, kuma ya dauki wannan matakin ne bayan da tsarin mulkin kasar ya amine masa da yin haka saboda yana ganin tsufa da rashin lafiya sun hana shi sauke nauyin da ya rataya a kansa.

Bayan kwana daya da saukarsa ne dansa Naruhito ya dare gadon sarautar Chrysanthemum, inda ya bude wani sabon babi a tarihin dadaddiyar kasar da ke yankin Asiya.

A Japan, sarki ba shi da wani iko na mulki amma wata alama ce ta hadin kan kasar.

A tsawon lokacin da ya ke rike da sarautar, Sarki Akihito ya zama abin so ga al’ummarsa saboda yadda ya rika kula wa da masu fama da cututtuka da matsalolin rayuwa kamar girgizar kasa da amabaliyar ruwa.

Sabon sarkin zai kasance sarki na 126 a jerin sarakunan Japan.

Shekarunsa 59 da haihuwa, kuma ya halarci Jami’ar Odford ta Ingila kafin ya zama yarima mai jiran gado tun yana da shekara 28 da haihuwa.

A shekarar 1986 ya hadu da matarsa Gimbiya Masako Owada, kuma sun yi aure a 1993.

Suna da ’ya daya tilo mai suna Gimbiya Aiko, wadda aka haife ta a 2001.

Amma dokar kasar Japan ta haramta wa ‘ya mace gadon sarautar kasar, saboda haka ba za ta gaji mahaifinta ba ke nan.

Kawun Gimbiya Aiko ne Yarima mai jiran gado na farko, sai kuma dansa Yarima Hisahito wanda yaro ne mai shekara 12 da haihuwa.

Yadda gidan sarautar Japan ya kasance daga 1901 zuwa yau. Maza ne kawai ke iya gadon sarauta, kuma ana fargabar zuwan ranar da babu namijin da zai gaji sarautar kamar yadda BBC ya ruwaito.

Bikin sauka daga sarauta

Abu na farko da sarki Akihito ya yi cikin shirin sauka daga sarautar shi ne na ziyarta wurin bauta na addinin Shinto, inda ya sanar da wadanda suka gabace shi a fagen sarauta cewa ya yanke shawarar sauka daga mulki.

An fara kuma aka kammala bikin ranar Talatar da ta gabata, kuma wannan ne karon farko da duniya ta fara ganin yadda Sarki a Japan ke sauka daga mulki.