✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon shugaban ‘yan sanda ka yi shirin magance magudin zabe -PDP

Kungiyar kamfe na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP (PPCO)  ta bukaci sabon Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya na riko, AIG Abubakar Adamu…

Kungiyar kamfe na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP (PPCO)  ta bukaci sabon Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya na riko, AIG Abubakar Adamu Muhammed da ya tabbatar sahihancin aikin hukumar ‘yan sandan Najeriya.

Daraktan sadarwa na kungiyar Kola Ologbondiyan ya bukaci sabon shugaban ‘yan sandan Najeriya da ya yi watsi da shirin da wasu ‘yan siyasa ke da shi na yin magudin zaben 2019.