✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranaku uku ne yanzu za a rika fita a Kano

An kara sassauta dokar hana fitar da aka sanya saboda coronavirus a jihar Kano zuwa kwana uku a duk mako. Za a bude wuraren ibada…

An kara sassauta dokar hana fitar da aka sanya saboda coronavirus a jihar Kano zuwa kwana uku a duk mako.

Za a bude wuraren ibada da kasuwanni da sauran harkoki a ranakun Laraba da Juma’a da kuma lahadi daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

Gwamnatin jihar ta wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba ya fitar ta gindaya sharuddan kasuwanni da wuraren ibada za su cika.

Umurnin ya wajabta rufe fuska, da samar da abun wanke hannu da kuma auna yanayin zafin jiki a wuraren ibada da kasuwanni.

Hakan ya biyo bayan ganawar da gwamnatin jihar ta yi ne da shugabannin addinai da ‘yan kasuwa da kwararru a fannin lafiya.

Sai dai kuma makarantu za su ci gaba da zama a rufe a fadin jihar, kazalika sufuri tsakanin jihar Kano da wata.

Gwamantin jihar ta shawarci ‘yan makaranta da su rika bin darussan da ake sakawa a gidajen radiyo ta talabijin loto-loto a jihar.