✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1441 (BH): Kalubale ga al’umma da matasa

A wannan mako GIZAGO (08065576011) ya yi nazari ne tare da tsokaci dangane da muhimmancin Shekarar Musulunci (Hijiriyya) ga al’umma. Shin me ya kamata mutum…

A wannan mako GIZAGO (08065576011) ya yi nazari ne tare da tsokaci dangane da muhimmancin Shekarar Musulunci (Hijiriyya) ga al’umma. Shin me ya kamata mutum ya yi, yayin da Allah Ya ba shi ikon shiga sabuwar shekara? A biyo mu:

A Lahadin da ta gabata ce muka shiga sabuwar Shekarar Musulunci ta 1441 (Bayan Hijira), don haka muke taya dimbin masu karatunmu barka da shiga sabuwar shekarar lafiya. Wannan ya nuna mana cewa, rayuwa na nufin shudewa daga wani zango zuwa wani, domin watanni goma sha biyu da suka gabata sun yi mana ishara da haka. Wannan dalili ne ya sanya muka ga ya dace mu yi tsokaci game da taken maudu’inmu na yau da ke sama, wato game da rayuwar al’umma, musamman  sinadaran da al’umma ke bukata domin tunkarar kalubalen da wannan shekara ta bijiro mana da su a rayuwa.

Babu shakka, mutum bai yi kabba ba, bai yi katobara ba kuma bai kwafsa ba, idan ya dauki wannan maudu’i na yau, ya nazarce shi da idon basira. Wannan zai ba mutum damar daura damarar tunkarar al’amuran rayuwa gadan-gadan. To, amma idan muka dubi kanun maudu’in, mun ambaci al’umma gaba daya, sai dai kuma za mu fi karkata akala ga matasa. Ko me ya sanya? Ga dalili:

Matasa ne aka yi ittifakin sun fi kowa yawa a yau, kuma su ne mafiya muhimmanci wajen fuskantar rayuwa, haka kuma su ne akasari suke yin nadama da da-na-sanin daukar wani mataki na rayuwa. Matasa ne kan fuskanci babban kalubalen da ke sanyawa ko dai su samu nasara ko su fadi warwas. Dalili ke nan ya sanya za mu yi amfani da wannan lokaci, domin zizara musu wani dan sinadari na rayuwa, domin mu kara musu kaimi,  mu tada su daga barci, idan barcin suke yi.

A lokacin da muka shiga wannan sabuwar shekara ta Hijiriyya ta 1441, akwai bukatar matasa su tsaya da ransu, su natsu, su gane muhimmancin lokaci, su daina bata lokaci wajen gudanar da wasu ayyuka ko al’amura marasa tasiri, wanda yin haka babu abin da zai amfane su da shi sai asarar rayuwarsu. Masu hikima dai sun ce lokaci dukiya ne, duk wanda ya bata shi, ya bata rayuwa.

Idan mun lura da yadda matasanmu suka shantake kuma suke bata lokacinsu wajen gudanar da wasu abubuwa marasa tasiri ga rayuwa, lallai akwai bukatar a yi musu tambihi, domin ankarar da su, su bi turbar da ta dace.

Ta wace hanya ce matasa za su ci gajiyar lokacinsu a cikin wannan shekara ta Hijira da Allah cikin ikonSa muka shigo? Na farko dai, yana da kyau mutum ya raba lokacinsa zuwa gida-gida kuma daki-daki, sannan ya aiwatar da al’amuransa bisa jagorancin tsarin da ya yi wa lokacin nasa. Misali, a wannan zamanin, babu abin da ya kamaci matashi kamar neman ilimi. To, kuma ba neman ilimi ne kadai rayuwa ba, don haka sai matashi ya tsara lokacin karatu da lokacin neman wasu abebadai na rayuwa.

A nan ya kamata in jawo hankalin matasa, musamman masu bata lokacinsu wajen kallon kwallon Turawa, wanda illar haka har ta yi tasiri a rayuwarsu. Haka na haddasa rugujewar al’amuran matasa da dama. Misali, a wajen kallon kwallon nan, matasa kan shiga lokacinsu na hutu da  lokacin da za su tsinana wa kawunansu wani aiki na amfani. A wajen kallon kwallon nan, za ka ji ana gardama, wacce ba ta da sididi balle sadada.

Kwarai kuwa! Babu dalilin da zai sa matashi ya jajirce yana gardama game da wani mutum, wanda bai san ma shi matashin yana cikin duniya ba. Haka kuma, gardamar ba ta da amfani, domin ba wata karuwa ta ilimi ko dukiya da mutum zai samu a sanadiyyar ta ba. To, me ya yi zafi da mutum zai bata lokacinsa haka?

Wani lokaci ma, illar ba a gardamar kadai take tsayawa ba, abin na yin zurfi har ya kai ga fada. Fada ba karami ba, domin kan kai ga yi wa juna rauni, wani lokaci har da rasa rayuka. To, idan aka yi rashin dacen haka ta faru, mene ne amfanin wannan kallo, kuma mene ne matashin ya samu a sanadiyyar haka?

A lokacin da muka shiga sabuwar shekara, ya kamata matasa su maida hankali ga ayyukan ci gaba, su guji zaman kashe wando ko zaman maula. Babu abin da mutum zai amfana daga haka sai asara bisa asara. Kuma ina amfanin matashi ya wayi gari bai da abin yi sai  zaman tsegumi da maula? Mu tuna da cewa, wanda ya mike ya nemi sana’a komai kankantarta da za ta rufa masa asiri, ya fi ya zauna dashasha, sai wani ya nemo, sannan ya je yana make murya don a ba shi. Babu shakka wannan ba karamar illa ba ce ga rayuwa. Don haka, muddin matashi ya shiga sabuwar shekara da irin wannan kudiri, na cewa sai an ba shi na zaman kashe wando, to, lallai haka watannin nan goma sha biyu za su shude, ba tare da ya tsinana wa kansa komai ba.

Lallai akwai bukatar matasa su dauki babban darasi daga na gaba da su, musamman tsofaffi da ke raye da wadanda suka shude. Tasirin haka shi ne, domin masu iya magana sun ce, da na gaba akan gane zurfin ruwa. Duk wanda ya samu nasarar rayuwa ta fannin ilimi ko dukiya ko kuma rufin asirin rayuwa, akwai dalilin kasancewarsa haka. Domin a lokacin da yake kuruciya, babu shakka bai wulakanta kansa da lokacinsa ba. Ke nan ya yi amfani da lokacinsa yadda ya dace, wajen neman sana’a ko aiki; wanda haka ya sanya ya samu nasarar abin da ya sanya a gaba.

Don haka muna kira ga al’umma, musamman matasa, su fahimci cewa amfanin lokaci a rayuwa shi ke sa a ci gajiyar rayuwa. Su binciki ayyukansu da rayuwarsu na shekarar da ta wuce, sannan su yi nazarin turbar da za su bi a cikin wannan sabuwar shekarar ta 1441 Bayan Hijira, da nufin samun nasara a rayuwa. Allah Ya taimaka mana, Ya yi mana jagora a cikin wannan sabuwar shekara ta Musulunci, amin.