✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sace jama’a na saka manoma kaura daga yankin arewa – Inji ‘yan kasuwa

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na kasa, NANTS, Barista Ken Okaoha, ya yi gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya na zagwanyewa cikin hanzari, sakamakon yadda ake tilasta…

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na kasa, NANTS, Barista Ken Okaoha, ya yi gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya na zagwanyewa cikin hanzari, sakamakon yadda ake tilasta manoma barin yankin. Yankin da ya yi kaurin suna ta fuskar bunkasar harkokin noma.

A wata mukalar da ya gabatar, a wajen taron horarwa dan gano manufofin yadda manoma suke dukufa ga noma, Mista Okoaha, ya koka a kan yadda ya ce wasu ‘yan kasuwa daga wasu sassan kasar nan, ke kaucewa zuwa yankin na Arewaci, sakamakon fargabar yiwuwar a yi garkuwa da su.

Shugaban kungiyar, wanda babban jam’in kungiyar na shiyya ya wakilta, James A.M Sako, ya ce hare-haren da ake kai wa manoman ya haddasa raguwar amfanin gonar da ake samu a yankin. Don haka, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tashi tsaye wajen kare manoman daga hare-haren.

Ya kara da cewa a yanzu ‘yan kasuwa ma na cikin zullumi, ta yadda suka kasance suna tsoron hada-hadar kayayyakinsu zuwa kasuwanni daban-daban, sakamakon yawaitar sace mutane ana garkuwa da su. Ya ce matsalar tana cin dundunniyar harkokin kasuwanci dama safarar kayayyaki matuka, a cikin kasar nan.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da ka da su kara farashin kaya, kawai saboda karin albashin ma’aikata da gwamnati ta yi, a kwanan nan. Ya gaya wa ‘yan kasuwar cewa, kara farashin bai zama wajibi ba kuma rashin sanin ya kamata ne, ko kuma ma, rashin imani ne tsububu.

A nata tsokacin, shugabar sashen mata ta kungiyar, Hajiya Hadiza Abdulfatah ta yi kira ga mata da su rungumi sana’ar noma don kula da iyali, ta na mai cewa, zamanin mata su zauna a gida kawai don su ma su aure ne, yanzu ya kau.