✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sace yara a Kano: Sarkin Kano ya yi bayani

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a wajen wani taron hana shan miyagun kwayoyi na (LESPADA) da aka yi a birnin Kano. Yayin jawabin…

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a wajen wani taron hana shan miyagun kwayoyi na (LESPADA) da aka yi a birnin Kano. Yayin jawabin da Sarkin ya yi a taron, Sarki Sanusi ya ce, “Bayan mun samu rahoton sace yara, mun riga mun yi bayani tun da aka fara maganar yaran nan na Onitsha, muka yi magana da Obi of Onitsha, kuma muna sane da halin da ake ciki kuma da binciken da ake yi”.

“Amma kafin a zo kan wadanda aka ce sun sace mana yara, duk ana ta zage-zage, sun sace mana yara, mun ji sun yi laifi. Amma shin wanda ya saci yaron nan cikin gidanka ya shigo ya sace shi? Dole mun canza tunanin mu, mu daina dora laifi a kan wasu muna janyo matsaloli.

Sarkin, ya kara da cewa, “Ban ce masu garkuwa da mutane ba su da laifi ba, kafin a yi min mummunar fahimta. Iyayen yara ke da hakkin kula da yaran su da tarbiyar su.”