Safarar shanun sata daga Arewa zuwa Kudu na damunmu – Sarakunan Fulani

Wadansu sarakunan Fulanin a Jihar Oyo sun koka kan yadda ake safarar shanun sata daga Arewa ana samar masu maboya a garuruwan Kurmi, lamarin da suka ce kamata ya yi mahukunta su sanya ido sosai domin magancewa.

Sarakunan Fulanin sun ce ce kimanin wata guda an kawo wasu shanu garke biyu a tirela aka jibge su a yankin Ado Awaye da ke Karamar Hukumar Iseyin a Jihar Oyo.

Sarkin Fulanin Igaga a Jihar Oyo, Alhaji Salihu Kadiri ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da ya samu labarin zuwan shanun yankin nasu ya je wajen da aka jibge su don ya gane wa idonsa abin da ake ciki, inda ya ce suna zargin sahihancin inda shanun suka fito. “Amma muna taka-tsantsan a kowane lokaci don ba ma fata abubuwa da suke faruwa a Arewa su iso gare mu, don haka mahukunta su sanya ido,” inji shi.

Alhaji Bani Abubakar Janhuro na Fulanin Oke Ogun a Jihar Oyo cewa ya yi yana da tabbas cewa shanun da aka jibge kimanin wata guda a yankin na sata ne. Ya ce sun samu labarin cewa ’yan sandan da ke aiki a karkashin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari mai jagorantar  ayarin musamman na IRT ke bincike game da lamarin, sannan ya ce akwai bayanan da ke nuna cewa Shugaban ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya san da maganar shanun, kuma bayanin da suka samu shi ne akwai mutanen da aka kama game da lamarin. Ya ce ba sa jin dadin yadda lamarin satar shanun ke kara yin kamari.

Ya ce shanun da aka jibge su a yankin nasu an kawo su ne daga ’yankin Lesa Barba a Jihar Kwara kuma a lokacin da shugabannin Fulanin yankin suka isa wajen domin bin diddigin lamarin sai wadanda ke tafe da shanun suka fada musu cewa da umarnin ’yan sanda da Kungiyar Miyyati Allah aka kawo shanun wajen. Ya ce shanun iri daban-daban ne da suka hada da yakana, maza da mata da kankana.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta tuntubi Mataimakin Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Alhaji Hasaini Basso wanda ya ce ana zargin barayin shanu ne suka sato shanun daga Dansadau a Jihar Zamfara da wani yanki da ke tsakanin Jihar Kebbi da Jihar Neja yankin da ake kira Karambana. Ya ce akwai wani mutum da aka sace wa shanun wanda shi ne ya biyo sawunsu ya kuma gane 45 a cikinsu lokacin da barayin shanun suka boye su a garin Lesa Barba a Jihar Kwara. “Ni ban je ba amma an kira ni an fada min cewa lokacin da ya je ya shigar da koke a wajen ’yan sanda, an kira ni ta waya, sai na kira Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari na ce ya tura mana mutanensa daga Ibadan domin su yi bincike kan lamarin. Kuma zuwa yanzu shanun na hannunsu an kuma kama mutum shida da ake zargi da hannu a lamarin kuma yanzu shanun na karkashin kulawar yaran Abba Kyari inda duk lokacin da aka samu masu shi mutum yakan zo da shaidunsa da takardar rantsuwa ta kotu sannan a tantance shi ya gwada nasa sai a ba shi. Akwai tsarin da suke bi su tantance, yanzu haka ina Kaduna. Irin wannan lamari ya yi kamari, yana faruwa a koyaushe, don haka nake kira ga mutanenmu su rika kula duk wanda aka ga ya shigo da shanun da ba a sansu ba, to su yi bincike har sai an gano asalin inda ya zo da shanun an tabbatar nasa ne. In ba haka ba batagari za su ci gaba da satar dukiyar jama’a suna kai ta wani yankin,” inji shi.

Ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shi ne yawancin masu sa-kai a irin wannan domin kare satar shanu da jama’a, gwamnati ba ta ba su kulawa ba ya ga dan taimakon da Kungiyar Miyetti Allah ke ba su. “Sai dai abin da dan dama-dama domin gwamnatocin Arewa na taimakonsu daidai gwargwado.”

Ya ce muddin ana so a magance matsalar, ya kamata matasan Fulani makiyaya su koma ga tsohuwar al’adarsu da aka sani, su daina shiga al’amuran da ke bata wa al’ummar Fulani suna, “domin a yanzu suna bata mana suna, kuma wannan abu babu dadi,” inji shi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya