✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (7)

Sayyidina Sa’idu, ya sadaukar da dukan rayuwarsa ga hidimar addinin Musulunci. Yayin da ya yi kaura zuwa Madina tare da sauran Musulmi, Manzo Allah (SAW)…

Sayyidina Sa’idu, ya sadaukar da dukan rayuwarsa ga hidimar addinin Musulunci. Yayin da ya yi kaura zuwa Madina tare da sauran Musulmi, Manzo Allah (SAW) ya hada shi ’yan uwantaka da Rafi’u dan Maliku Az-Zurki, mutumin Madina. Ya halarci dukan yake-yaken daukaka Musulunci tare da Annabi (SAW) in ba da Yakin Badar. Shi ma, Manzon Allah (SAW) ne ya tura shi, ya gano karfin rudunar kafirai shi da Sayyidina Dalhat (RA).

Sayyidina Sa’idu, ya samu babban matsayi a wurin Manzon Allah (SAW). Ya ja shi a jika ya kusantar da shi shi zuwa gare shi, ya kuma yi masa bushara da gidan Aljanna. Ya yi wafati (Manzo SAW) yana yardajje a gare shi. Sa’idu (RA) ya nuna jarumtaka sosai a sauran yake-yaken yada Musulunci a zamanin Khalifa Abubakar da Umar (Allah Ya yarda da su), musamman Yakin YARMUK da na Bude Damaskus. Bayan samun nasarar Musulmi, sai Abu Ubaida, (Jagoran Yakin) ya sanya shi, ya zama Gwamnan Musulunci na farko a birnin (Damaskus).

Sayyidina Sa’idu (RA) mutum ne mai son zuriya da yawa. Malaman tarihi sun ambaci cewa ya haifi ’ya’ya 31, maza 13, mata 18. Allah Ya ba shi tsawon rai. Domin ya ga zamanin Mu’awiyya (Daular Banu Umayya). Ya kasance mai karbabbiyar addu’a.

Akwai wata mace mai suna Arwaa ’yar Uwaisu da ta taba kai kararsa wurin Marwanu dan Hakamu, Gwamnan Madina (na Daular Banu Umayya) ta ce wai ya kwace mata wani yanki na filinta, ya hada cikin nasa. Da Marwan ya aika masa kan wannan magana, sai mamaki ya kama shi. Ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kwaci wani fili gwargwadon taki guda, Allah zai sanya shi daukar kassai bakwai Ranar Alkiyama.” Sai ya ba ta fili, gwargwadon abin da ta ce ya kwace mata, sannan ya yi addu’a, ya ce: “Ya Ubangiji! Wannan  mace, ta yi da’awar cewa, na zalunce ta. To, idan karya take yi, (Ya Allah!) Ka makantar da ita, ka kuma jefa ta cikin rijiyar gidanta.” Sai kuwa Allah Ya amshi wannan addu’a tasa. Ba a dade ba, wannan mata ta makance. Wata rana kuma tana kewayawa a cikin gida sai ta fada rijiyar gidan nata ta rasu.

Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: “Lokacin muna yara idan an zalunci wani mutum, mukan ji ya ce da wanda ya zalunce shi “Allah Ya makantar da kai kamar yadda ya makantar da Arwaa.”

Sayyidina Sa’idu (RA), ya rasu rana Juma’a Hijira na da Shekara 51, yana da shekara 73. Abdullahi dan Umar da Sa’idu dan Abu Wakkas su ne suka jagorance binne shi. (Allah Ya kara masa yarda).

  1. Abu Ubaida bin Jarrah

“Kowacce al’umma tana da amintacce. Amintaccen wannan al’umma, shi ne Abu Ubaida.”

Shi ne Abu Ubaida, Amiru dan Abdullahi dan Jarrah. Bakuraishe. Bafihire (daga zuriyar Banu Fihiri). Daya daga cikin Musulmin farko kuma daya daga cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gida Aljanna wadanda Manzon Allah (SAW) ya yi wafati suna yardaddu a gare shi. Yana daga cikin abokan Sayyidina Abubakar (ra) wadanda ya kira su zuwa ga Musulunci.

Yana cikin Musulmin farko da suka sha fama da kiyayya, gami da cuta da zalunci iri-iri daga kafiran Makka. Yana kuma cikin rukuni na biyu, na Musulmin da suka yi kaura zuwa kasar Habasha. Ya kuma yi kaura tare da sauran Musulmi zuwa Madina. A can ne Manzon Allah (SAW) ya hada shi ’yan uwantaka da Sa’adu dan Mu’azu mutumin Madina.

A Yakin Badar, Sayyindina Abu Ubaida (RA) ya fatattaki gayyar kafiran Makka. Duk kafirin da ya tsaya gabansa sai dai wani ba shi ba. A wannan a rangama ce ta filin Badar mahaifinsa da ke cikin rundunar kafirai ya tare shi. Abu Ubaida (RA) bai saurara masa ba, nan take ya aike da shi zuwa Lahira! Saboda irin wannan karfin imani na Musulmin farko irin su Abu Ubaida, Ubangiji Ya saukar da fadinSa:

“Ba za ka samu mutane masu yin imani da Allah da Ranar Lahira, suna yin soyayya ga wanda ya saba wa Allah da ManzoSa ba, ko da sun kasance iyayensu ko ’ya’yansu ko ’yan uwansu ko danginsu. (Irin wadannan mutane) Allah Ya rubuta imani a zukatansu, Ya karfafe su da ruhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su Aljanna, wadda koramu ke gudana a karkashinta, suna masu dawwama a cikinta. Allah Ya yarda da su ma sun yarda da Shi. Wadannan, su ne Rundunar Allah to, lallai kuwa Rundunar Allah su ne masu rabauta.” Suratul (Mujadala: 22).

A Yakin Uhudu kuwa yayin da kafirai suka tarwatsa rundunar Musulmi, Sayyidina Abu Ubaida (RA) yana cikin tsirarun sahabban da suka tsaya, don kare Annabi (SAW). Haka kuma ya halarci dukan yake-yaken jihadi tare da Manzon Allah (SAW) cikin kowane yaki. Kuma, yakan yi dauki-ba-dadi sosai, wajen kawar da makiya Allah da tabbatar da addinin Musulnci. Sayyidina Abu Ubaida (RA), babban jarumi ne, na a-zo-a-gani. Don haka kafirai suke shakkar karo da shi. Manzon Allah (SAW), ya ce: “Kowace al’umma tana da amintacce. Amintaccen wannan al’umma, shi ne Abu Ubaida.”

Sayyidina Abu Ubaida (RA), mai zuzzurfan ilimi ne, a sha’anin addinin Musulunci. Mai nagartaccen ra’ayi a fanin siyasa. Mai zurfin hikima a lokacin tsanantuwar lamura. Cikakken barde a fagen yaki, ya yi bajinta sosai a Yakin YARMUK. Kuma shi (Abu Ubaidu) Khalifa Siddiku (RA) ya nada shugaban rundunonin Musulmi, a wannan yaki. A karkashin jagorancinsa, Musulmi suka samu nasara, a mashahurin yakin nan na KADISIYYA da sauran manyan garuruwa na kasar Sham.

Sayyidina Abu Ubaida (RA) ya rasu sakamokon wata annoba da ta samu rundunar Musulmi da yake yi wa jagoranci a Falasdinu a shekara ta 18 dage Hijira zamanin Khalifa Umar dan Khaddabi (RA).  Allah Ya kara masa yarda.

Wannan shi ne abin da Allah Ya nufe mu da tarawa na tarihin wadannan sahabbai goma da suka samu busharar shiga Aljanna tun suna raye. Muna rokon Allah Ya ba mu ikon koyi da halayensu kyawawa. Amin

Imam Ahmad Adam Kutubi,

Nigeria Police Force,

Zone 7, Police Headkuarter,

Abuja. 08036095723