✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai an biya barnar da masu #EndSARS suka yi mana

Masu sana’o’i sun bukaci a biya su diyyar barnar da aka yi musu a zanga-zangar #EndSARS.

Kungiyoyin masu sana’o’i sun bukaci a biya su diyyar barnar da aka yi musu a zanga-zangar #EndSARS a sassan Najeriya.

Kungiyoyin man fetur, sufuri, manoma da sauransu na neman gwamnati ta biya su motoci, amfanin gona, rayuka da sauran abubuwan da aka salwantar a lokacin zanga-zangar.

“Muna kira da murya daya ga gwamnatoci a dukkan matakai su gano su kuma biya diyya ga duk wadanda aka lalata wa motoci, kaya, amfanin gona ko kadarori, ko aka sace ko halakawa domin a rage musu radadi”, inji kungiyoyin.

Bayan la’antar barnar da aka yi musu, kungiyoyin sun kirayi gwamnati a dukkan matakai ta gano, tsare da kuma hukunta masu hannu a sace-sace, kone-kone, kashe-kashe da jikkata mutane da bata-gari suka yi a lokacin zagan-zagar ta watan Oktoba.

“Dukkannin matakan gwamanti su mike su yi aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Najeriya.

“Gwamantin Tarayya ta matsa kaimi a yakar ’yan bindiga, masu garkuwa, ’yan fashi da ’yan ta’adda baya domin mutane su rika yin harkokinsu cikin aminci”, kamar yadda suka bukata.

Sun koka cewa zanga-zangar #EndSARS koma tashin hankali musamman a yankin Kudu, inda ake kai wa motocin fasinja, daukar dabbobi, mai da kayan abinci hari ana sacewa ko konawa; direbobi da yaran mota kuma ana kashewa ko lahanta su.

Don haka suka roki Gwamnatin Tarayya, jihohi, kungiyoyi da hukumomin duniya sukawo musu tallafi domin saukaka musu tasirin irin asarar da suka yi.

Sun bayyana damuwa kan farmaki da ’yan daba kan kai wa direbobi, motoci da sauran dukiyoyi da suna zanga-zanga har ta kai ga kisa bayan lalata dukiyoyi.

Kungiyoyin sun hada da PTD ta direbobin tanka, ma’aikatan man fetur, RTEAN na ma’aikatan sufuri, AUFCDN ta dillalan kayan abinci da dabbobi, AFSGSAN ta masu hatsi da manoma.