Da Dumi Dumi

Sai Buhari ya bar mulki zai san wadanda suka cutar da shi – AB Kwaccham

Shugaban Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas ta Mobement of North East Youth Forum, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham, ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalolin tsaro ta hanyar magance cin hanci a tsakanin shugabannin sashin tsaron. A.B Kwaccham ya ce akwai bukatar Shugaban Kasa ya binciki zargin rashin isar wasu kudaden alawus da ake ware wa jami’an tsaro musamman wadanda ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas.

“Su kuma masu aikata haka su kwana da sanin cewa ko bade-ko ba jima za su fuskanci bincike bayan Shugaba Buhari ya bar mulki lokacin da zai gane cewa sun cutar da shi,” inji shi.

“Ba daidai ba ne wanda aka yaba wa iya Sallah ya kasa alwala. Abin da ke faruwa na zubar masa da mutunci da kima a wajen masoyansa na ainihi wadanda suka zabe shi don ya magance matsalar. Dole ne a kawar da son kai a sama wa lamarin maslaha ta hanyar sauraron korafi da shawarwarin jama’a. Ba daidai ba ne duk abin da Shugaba ya tsara wa kansa a ce ba zai sauya ba koda hakan ya gaza yin abin da a ke bukata,” inji shi.

Shugaban matasan ya bukaci a dawo da jami’an tsaro na sa-kai musamman a Karamar Hukumar Mubi da ke Jihar Adamawa yankin da ya fito, inda ya ce lokacin da aka yi amfani da su a baya, an samu sauki kan matsalar sace jama’a da wadansu ke yi suna neman kudin fansa, inda ya ce yanzu matsalar ta sake kunno kai a yankin.

“A lokacin da suke aiki idan suka kama wanda ake zargi, mutum da kansa zai yi ta furta laifuffukan da ya aikata sannan a zantar masa da hukunci nan take. Sai aka samu wadansu miyagu suka rubuta korafi ga kungiyoyi da ke ikirarin kare hakkin dan Adam, yanzu ga shi matsalar satar jama’ar ta sake dawowa a yankin,” inji Kwaccham.

ADVERTISEMENT

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya