✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai da na rage albashi domin in koma Man. United – Ighalo

Dan asalin Najeriya Odion Ighalo ya ce ya kagu ya koma Manchester United, domin tun yana yaro yake son kungiyar, wanda hakan ya sa ya…

Dan asalin Najeriya Odion Ighalo ya ce ya kagu ya koma Manchester United, domin tun yana yaro yake son kungiyar, wanda hakan ya sa ya rage albashinsa don samun  zuwa Old Trafford ya taka leda.

Dan wasan ya ce ya yi matukar farin ciki da aka amince ya yi wa United wasa a matsayin aro, kuma ranar bai yi barci ba saboda murna.

Dan wasan mai shekara 30 wanda aka aro daga Kungiyar Shanghai Shenhua ta China zai yi wa United wasanni ne zuwa karshen kakar bana.

Tsohon dan wasan na Watford ta Ingila ya ce mahaifiyarsa har kuka ta yi don murna, kuma sai da aka yi biki a kan titin da ya girma.

Ya ce kungiyoyi da dama sun yi zawarcinsa, amma zuciyarsa ta ce masa ya zabi Manchester United.

Ighalo ya ce da tsakar dare manajansa ya shaida masa cewa United na son daukarsa, inda ya kara da cewa nan da nan bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi mai fassara harshe suka dunguma zuwa ofishin Daraktan Kungiyar Shanghai Shenhua. Daga nan ne Ighalo da wakilinsa suka kwashe tsawon dare wajen kulla yarjejeniya da cike takardun ka’ida da sa hannu kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ’yan kwallo ta watan Janairu.