✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai masoya Buhari sun biya zan saki sabuwar waka —Rarara

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ayyuka da dama domin ci gaban Najeriya. Mawakin ya bayyana…

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ayyuka da dama domin ci gaban Najeriya.

Mawakin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo, inda ya ce ya rera wa Shugaba Buhari sabuwar waka mai suna Kainuwa domin bayyana wa duniya wasu ayyuka 92 da shugaba ya yi.

Sai dai mawakin ya ce ba zai saki wakar kyauta ba, sai masoyan Buhari sun biya.

Rarara ya kara da cewa dalilin da ya sa masoyan Buhari za su biya shi ne ganin yadda wasu mutane suke cewa farin jinin Buhari ya dusashe, wanda a cewarsa ya sa suke so masoyan na Buhari su fito su nuna.

“Kowa zai biya Naira dubu daya. Wannan zai ba da tabbacin masoya Buhari suna nan”.

Rarara ya dan rera wakar, inda a ciki yake cewa: Shi dai Buhari sunansa kainu…

Dan Adam na da mantuwa…