Aminiya

Sai mun cimma matsaya da kasashe makwabta kafin bude iyakokin Najeriya- Shugaban Kwastam

Shugaban hukumar hana fasakwabri ta kasa (Kwastam) Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya jaddada aniyar kasar nan na kara dage dantse domin kula da iyakokinta. Inda ya ce, shirin nan na musamman da a yanzu ke gudana akan iyokokin kasar nan na haifar da mai ido. Ya ce a yanzu babu takamaiman ranar bude kan iyakokin Najeriya domin shige da ficen kayayyaki, “Zamu sassauta ne kadai idan muka zauna da makwabtan kasar mu muka cimma yarjejeniya sannan suka bi ka’idojin da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta kafa sannan ne zamu sassauta.”

Ya ce, ba kamar yadda wasu ke yadawa ba cewa za a bude iyakokin bayan kwanaki 28, “mun yi shirya tsarin bisa matakai, kwanaki 28 su ne mataki na farko dan haka zuwa yanzu babu wani kayadajjen lokacin bude iyakar har sai mun cimma matsaya da makwabtan mu.”

ADVERTISEMENT

Kanal Hamid Ali, ya shaida hakan ne a sa’ilin rangadinsa a kan iyakar Najeriya da kasar Benin a yankin iyakokin Same a Legas da Idiroko a jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gabata inda ya shaidawa Aminiya cewa, izuwa yanzu an samu bunkasar tsaro da tattalin arziki kasa biyo bayan matakan da aka dauka akan iyakokin Najeriya.

ADVERTISEMENT