✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sajan sama ya mutu lokacin atisaye a Kaduna

Rundunar sojan saman Najeriya (NAF) ta sanar da rasuwar jami’in ta daya da ya mutu lokacin atisaye da ake yi masu a Kaduna. Kakakin rundunar…

Rundunar sojan saman Najeriya (NAF) ta sanar da rasuwar jami’in ta daya da ya mutu lokacin atisaye da ake yi masu a Kaduna.

Kakakin rundunar sojojin sama Iya Kwamando Ibikunle Daramola ne ya sanar da hakan, inda ya ce, Kofura Meshach Iliya Komo ya mutu ne jiya a Kaduna lokacin da suke atisayen sauka kasa daga jirgin saman.