✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saka jakar mata ta raba ni da bara – Ibrahim Makaho

Malam Ibrahim Ahmad makaho ne da ya zabi yin sana’ar sake-saken zamani a Unguwar Kama-Wuri-Zauna da ke kusa da Kasuwar Kifi, Kado-Abuja. Ya yi wa…

Malam Ibrahim Ahmad makaho ne da ya zabi yin sana’ar sake-saken zamani a Unguwar Kama-Wuri-Zauna da ke kusa da Kasuwar Kifi, Kado-Abuja. Ya yi wa Aminiya bayani a kan yadda ya ajiye yawon bara ya rungumi sana’a da kuma irin burin da yake da shi a gaba.

Shin ina ne asalinka, wato garin da ka fito?

Sunana Ibrahim Ahmad kuma an haife ni a wani kauye mai suna Rubun a Karamar Hukumar Albasu ta Jihar Kano. A yanzu ina da shekara kamar 30 a duniya.

Wannar makanta, shin da ita ce aka haife ka ko dai daga baya ne ta same ka?

Na gamu da larurar makanta tun ina da shekara biyar, a sakamakon ciwon kyanda. Iyayena sun yi mini jinya a bangaren asibiti da kuma maganin gargajiya amma daga karshe sai suka hakura bayan ido guda ya kumbura sannan ya tsiyaye. Sai dai dayan yana nan haka bai tsiyaye ba duk da dai ko haske ba na iya gani da shi.

An kai ni makarantar allo a garin Takai ina da shekara 9 sai kuma a Duja. To daga baya sai na fara tafiya da kaina har na je Maiduguri. A can na yi saukar Alkur’ani ta daya, na kama hanyar ta 2 sai dai ban kai ga karasawa ba sai na ajiye karatun kamar shekara 4 da ta wuce; bayan an yi mini aure. To daga nan ne kuma sai na koma neman kudi kadai ta hanyar bara, ina fita ina komawa. Alhamdu lillahi, a yanzu ina da ’ya’ya 2 da na samu da matata.

Yaushe ka zo nan yankin Abuja?

Na zo Abuja a shekara ta 2004, inda na fara bara, har kuma na zo ina sayen waya ta hannu, idan kamar mutum ya shiga hali na matsuwa, ina sayarwa idan na samu riba. To kamar shekara 2 da suka wuce sai na shiga wannan sana’a ta sakar abubuwan amfanin mata da duwatsu.

Ko me ya karfafa maka gwiwa ka rungumi sana’ar, duk da cewa kai makaho ne?

Na hadu da wani a nan Abuja da ya koyi aikin a makarantar makafi ta Ikeja da ke Legas, mai suna Usman Abdullahi. Makaho ne kamar ni, to abin da yake yi ne ya karfafa mini gwiwa kuma bayan na bayyana masa sha’awata a kan hakan, sai ya koya mini. Da farko na koyi aikin wannan abu da ake kira da ‘Ma’ajin Fulawa’ (flower base) a wurinsa, samfurin mai lankwasa 4.

To daga baya sai na fara yin mai lankwasa 6. Haka na yi ta fadada aikin da kaina har na koyi jakar mata da kuma shimfidar tebur sai kuma abin saka takardar goge najasa (Toilet Paper), wanda ake ajiyewa a cikin mota.

Kamar wane tsawon lokaci kake yi wajen hada guda daya?

Nakan sayo kayan aikin guda 2 ne, kasancewar ba ni da isasshen jarin sayen mai yawa. Nakan kammala saiti biyun a cikin kwana 3, sai in sayar in samu kudin sayo wasu kayan aikin; abin da ya hau sama shi ne matsayin ribata kuma a ciki ne nake ci da kuma biyan sauran bukatun iyali.

Kamar wadanne abubuwa ne ake bukata wajen kera kayayyakin naka?

Abubuwan da ake bukata ba su wuce 3 ba. Na farko shi ne duwatsu (beads), wanda za a bukaci launuka 2, kowace jakar ledarsa wanda bai wuce girman ledar magi ba, ana sayar da shi ne a kan Naira dubu daya da dari biyar; sai dai a wani wajen yana kaiwa Naira 1,800. Sai kirtanin roba da ake kira “fishing line,” ina sayen kwallonsa guda a kan Naira dari biyar. Shi ko adon fulawa da ake sakala shi a sama, ana sayar da shi ne a kan Naira dubu daya. Idan kuma babba ne don aiki na musamman, yana kaiwa har Naira dubu daya da dari biyar, saboda a wani zubin akan ba ni aiki na musamman tare da bukatar karin girma da kuma launuka. Amma dai ni a kashin kaina, na fi yin mai girman, irin wannan da ka same ni da shi, wanda na ke sayarwa a kan Naira dubu hudu, idan kuwa na sa masa fulawa, na sayar Naira dubu biyar.

Wace hanya kake bi wajen ganin ba a sami akasi ba kasancewar kana amfani da launuka mabanbanta?

Kamar yadda na yi maka bayani, ina sayan ledar duwatsu guda uku ne wajen saka jakunkuna biyu. Launin da zai fi yawa ina sayan ledarsa guda biyu sai kuma wanda zai zama surki, in sayi leda daya. To dabarar da nake amfani da ita, ita ce, ina buda bakin ledar launin da zan yi amfani da shi a ratsi tun daga lokacin da mai sayarwa ya mikamin shi, ta hanyar jan bakin ledar sai ta fi fadi. Idan kuwa na fara aiki da ledar sai in yi kulli a jikinsa, ta yadda duk lokacin da na tashi bukatarsa, na san na aikin ratsi ne. Hakan ya taimaka mini da dogaro da kaina wajen sanin launi sannan kuma koda da tsakar dare ne na farka, sannan na ji yi sha’awar ci gaba da aiki zan yi aikina gaba-gadi kafin sake komawa barci.

Ko kana samun gamsuwa ta fuskar samun ribar da ta wadace ka?

Alhamdu lillahi, ana samun na biyan bukata da kuma rike iiyali. Sai dai a wani zubin akan samu lokaci kamar mako guda kafin in samu nasarar sayar da biyun gaba daya da na yi bayan na gama. Dama nakan zagaya masallatai ne sai kuma na gabatar da su ga jama’a bayan idar da Sallah daga gefen masallaci. A wani lokacin sai wani ya ba ni sautu ya ce a yi masa kamar kaza, wani zubin kuma yawatawa nake yi kamar mai talla; idan na sayar sai in sayo wasu kayan aikin.

Kamar wane irin ci gaba za ka ce wannar sana’a ta kawo maka?

Babban ci gaban da zan ce na samu shi ne, ina ci daga ciki sannan ina yi wa iyalina sako don biyan bukatunsu. Sai dai a ce an kai ga yin ajiya da nufin sayen wani abun amfani, gaskiya har yau ban kai ga yin hakan ba tukuna. Ta dai hana ni yawon bara.

Ya maganar kalubale kuma?

Babban kalubalen da nake fuskanta a wannar sana’a shi ne na rashin isasshen jari da zai ba ni damar sayen kayan aiki mai yawa don samun kwanciyar hankali ba tare da shiga halin takura ba. Saboda a yanzu idan na gama guda 2, ba dama in ci gaba da yin wasu har sai na sayar tukuna sannan in samu kudin da zan sayi wasu kayan aikin. To, a irin hakan ne a wani zubin sai ina shafe kamar mako daya kafin in samu nasarar sayar da biyun da na yi gaba daya. Albarkacin makafi ’yan uwana da nake tare da su ne nake rancen kudi a wajensu sannan idan na samu nasarar sayar da kayan sai in mayar masu da kudinsu.

Ko kana da wani buri da kake son ka cin mawa a gaba?

Babban burina a yanzu shi ne, wannan karatu na zamani da kusan kowa ke yi, ni ma na samu hanyar da zan bi in yi shi. Duk wadannan makafi da ka same ni tare da su a nan sun yi karatun boko, ni kadai ne a cikinsu ban yi ba. Dukansu nan dalibai ne wasu na matakin karatun sakandare wasu kuma suna manyan makarantu. Zama da su ne ni ma har na samu damar koyon wasu abubuwa a karatun kamar yadda su ma suke koyon wannan sana’a da nake yi. Abu na biyu kuwa shi ne, in inganta wannan sana’ar wajen koyon karin wasu abubuwan daban, a inda ake koyarwa. Dama wata shida ne ake yi sai a gama. Sai kuma in ga na kafa cibiya ta kaina don gudanar da sana’o’i irin wannan, inda zan zauna tare da sauran ’yan uwa a yi aiki.