✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saka na da zabin yi wa Najeriya ko Ingila kwallo – Arteta

Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Mikel Arteta ya ce Bukayo Saka da yanzu ke buga wa kulob din kwallo dan asalin Najeriya na…

Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Mikel Arteta ya ce Bukayo Saka da yanzu ke buga wa kulob din kwallo dan asalin Najeriya na da zabin yi wa Najeriya ko Ingila kwallo.

Saka wanda dan asalin Najeriya ne amma haifaffen Ingila yanzu haka tauraruwarsa na haskakawa a bana don kawo yanzu ya zura kwallo 4 kuma ya taimaka an zura wasu kwallo goma a raga.

Sai dai ana ta rade-radin kasar da dan kwallon zai zaba don ya buga mata kwallo.  A lokacin da aka nemi jin ra’ayin kocinsa na yanzu Mikel Arteta ya nuna ba shi zai zabar wa Saka kasar da ya dace  ya yi mata kwallo ba, don haka zabi ya rage nasa, ko dai ya zabi Najeriya ko Ingila amma lokaci ne kawai zai tabbatar da haka.

Jaridar Football London ta ruwaito Arteta na fadin duk kasar da Saka ya zabi ya mata kwallo zai mara masa baya. Yanzu haka Saka yana da shekara 18.