Aminiya

Sakamakon aikinku ne abin tsoro ba ni ba – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a jawabinsa na ranar ’yancin kai da aka watsa ta kafafen yada labarai, ya bayyana cewa gwamnmatinsa ba ta nufin cutar da kowa, sai dai kowa ya zama cikin shirin don bayyana abin da ya aikata.

ADVERTISEMENT

A jawabin nasa wanda ya gabatar, ya tunato da abin da ya fadi a ranar 29 ga Mayun bana, inda ya ce: “Ba ni da mugun nufi a kan kowa dangane da abin da ya faru a baya. Bai kamata wani ya ji tsoron wani abu daga gare ni ba
“Ba fakon wani muke yi ba. Mutane su ji tsoron sakamakon ayyukan da suka aikata. Na gayyaci kowa da kowa, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin siyasa ba, sai don mu hada karfi wajen yi wa kasa aiki.”
A yau Najeriya ta cika shekara 55 da samun ’yancin kai, bayan kasar Birtaniya ta ’yantar da ita a ranar 1 ga Oktobar 1960.
Shugaban kasar, ya ce, akwai bukatar ’yan kasa su yi murna, ba tare da yanayin da halin da muka tsinci kanmu ba, inda ya nuna takaicinsa ganin cewa, ba mu da manufar hadin kai mai ma’ana duk da cewa Allah Ya albarkaci kasar nan da yawan al’umma da albarkatun kasa.
Buhari ya bayyana cewa: “Muna da dukkan alamun da ke tabbatar da kasancewa hamshakiyar managarciyar babbar kasa. Mun kasa kai ga gaci ne, saboda gazawarmu wajen bin muhimmin mafarkin hadin kai mai ma’ana. Da tuni mun kai ga cimma managarcin tsarin siyasa da hadin kai, har da ci gaba da bunkasar tattalin arziki.
“kasashe masu karancin albarkatu sun samu bunkasar tattalin arziki da daidaituwar al’amura da hadin kai mai manufa.
“Duk da haka, kasancewarmu tare wata nasara ce da za mu yi murna da ita, mu kuma kara kaimin tarairayyarta.”
Sannan ya yaba wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya amince da faduwarsa a zaben ranar 28 ga watan Maris din 2015.
“Mun samu babban sauyi da ya bunkasa dimokuradiyyarmu a wannan shekarar. Ganin yadda jam’iyyar adawa ta maye gurbin gwamnati mai ci,a zabe mafi inganci, wanda ke nuni da cewa dimokuradiyyarmu ta samu kafuwa.
“Kowane irin ra’ayi mutum ke da shi, ’yan Najeriya dole ne su gode wa tsohon shugaban kasa (Goodluck) Jonathan da ya kauce wa rikici a lokacin da ya fadi zabe, al’amarin da ya ceto kasar nan daga fadawa matsanancin halin da ba a san makomarsa ba,” inji shi.
Da shugaban kasa ke bin kadin ayyukan da gwamnatinsa ta yi a tsawon watanni biyar da kama ragamarta, ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya na gaggawar ganin ya biya musu burinsu, don haka ya dauki matakan cimma wadannan burace-burace.
Buhari ya ce, “Kowace sabuwar gwamnati takan gaji dimbin matsaloli. Mu ma ba mu bambanta ba. Sai dai abin da ’yan Najeriya ke bukata, shi ne maganin matsalolin, wato warware su cikin gaggawa, sabanin a rika jero musu matsalolin da aka gada.
“Bisa tsari, bayan an tuntubi mataimakin shugaban kasa da shugabannin jam’iyya da sauran manyan masu ruwa da tsaki, na yi hanzarin dukufa wajen yin aiki ka’in da na’in, don shawo kan matsalolin na gaggawa da matsakaita da na dogon lokaci, al’amarin da ya zama dole mu warware su, matukar muna so ’yan Najeriya su ci gaba da samun kwarin gwiwa a kanmu, tun daga zaben da suka yi mana cikin watan Maris zuwa yanzu.
“Kamar yadda kuka sani, na jawo kasashen makwafta, inda muka jagoranci rundunar sojan kasashe biyar don tunkarar Boko Haram har ta kai ga mun karya lagon su. Sannan na gana da shugabannin kungiyar kasashe masu karfin masana’antu na “G7” da sauran shugabannin kasashen da ke kawance da mu, a kokarinmu na kafa rundunar duniya don farmakar Boko Haram.
“Zaratan rundunar sojojinmu, a karkashin sabon shugabanci sun tunkari maharan kunar bakin wake, inda suka yi rugu-rugu da motocinsu da makamansu. ’Yan Boko Haram sun tarwatse, inda wasu kuma ke gudun neman tsira.
“Sun fara kai hari a kan wuraren da aka tsugunnar da mutane masu rauni, wadanda suka hada da sansanin mutanen da yaki ya kore su daga garuruwansu, a manufarsu ta matsorata da ke son nuna karfinsu na nan. Don haka na umarci jami’an tsaro da na kananan hukumomi su tsaurara matakan tsaro a wuraren da ke tattare da fadawa cikin hadari.”
Shugaban kasar ya bayyana yadda jami’an gwamnati suka yi tattaunawa ta tsawon lokaci kan yadda za a bunkasa harkar samar da wutar lantarki a kasar nan, bisa tsari mara hadari da saukin kashe kudi, ta yadda aka samu nasarar samar da wutar lantarkin a kai-a kai.
Shugaban kasar ya yi nuni da cewa, an samu ingantuwar al’amura wajen samar da man fetur da kananzir ga al’umma, kuma alamu na nuni da cewa nan ba da dadewa, daukacin kasar nan za samu sauyi mai alfanu.
Kuma Buhari ya ce, an dauki matakan yi wa Kamfanin Man fetur na kasa garanbawul, don kawar da rashin nagarta da cin hanci.
“Wasu daga cikin matatunmu da za a iya gyara su, har su dan fara aiki, za su dawo bakin aiki, ta yadda za a kawar da cuwa-cuwar hada-hadar fitar da gurbataccen man fetur da kuma shigo da wanda aka tace, inda za a taka wa masu almundahana burki,” inji shi.
Shugaban kasar ya ce, ya bayar da umarni a gudanar da binciken kudin hukumomin gwamnmati da ke samar da kudin shiga, musamman wadanda suka hada da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar tara Haraji ta Tarayya (FIRS) da Hukumar Hana Fasakwauri ta Najeriya (NCS) da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta yadda za su rika aiwatar da managartan ayyuka ga kasa.
Jawabin shugaban kasar ya ci gaba da nuna cewa:”Akwai bukatar kyakkyawar kulawa fiye da kowane lokaci, musamman bisa la’akari da faduwar farkashin man fetur a kasuwar duniya. Wannan kalubale ne da za mu yi himma wajen tunkararsa. Sai dai abin lura a nan ba shi ne ba abin da ake Tarawa ba, illa dai kawai shi ne yaya muke ririta albarkatunmu ne muhimmi.
“Mun ga yadda aka ki ririta dimbin albarktu a ’yan shekarun da suka gabata, al’amarin da ya kai ga ana salwantarwa da kuma lalata dimbin dukiya. Wannan gwamnati ta jam’iyyar APC ta kuduri aniyar gyara, ta hanyar kula da binciken yadda ake kashe kudin al’umma.
“Da farko Gweamnatin Tarayya, ta yi kokarin warware matsalar albashin da ma’aikata ke bi a wasu jihohi, al’amarin da ya kusa haifar da tashin-tashinar yajin aiki. Gwamnatin APC ta shiga tsakani wajen warware matsalar na wucin-gadi, inda aka bayar da tallafi ga jihohin da ake bi bashi, don biyan albashin baya da tabbatar hanyar neman abincin miliyoyin ’yan Najeriya.
Sannan shugaban kasar ya yi magana game damuwar mutane dangane da jan-kafar da ya yi wajen nada ministoci. Ya ce gwamntinsa ta zabi kin yin gaggawar kafa majalisar ministoci ne ba tare da ta tantance hakikanin abin da gwamnatin da ta gabata ta bar mata ba.
A cewarsa: “Gwamnatinmu ta fito da managarcin tsarin wajen yin abin da ya dace. Mun karbi bayanan mulki daga gwamnatin da ta shude kwanaki hudu gabanin karbar ragamar mulki. Sakamakon haka Kwamitin Ahmad Joda ana karbar mulki ya mika rahotonsa kan yadda za a daidaita tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya bayan nazarin bayanan karbar ragama.
“Da tuni al’amura sun rincabe da an bayyana ministoci, kafin gwamnati ta tantance yawan ma’aikatun da za su iya daukar dawainiyar nauyin da ya rataya a harkokin mulki.
“Duk da haka, jan kafar ya kare. An tura rukunin farko na wadanda za a nada ministoci don majalisar dattawa ta tabbatar da su. Za kuma a tura sauran jerin sunayen a lokacin da ya dace.”
Sai dai shi Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewa, a ranar Larabar da ta wuce ya karbi jerin sunayen ministocin daga shugaban kasa, sannan majalisa za ta yi zaman tantance su ne a ranar Talata mai zuwa.

ADVERTISEMENT