✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakamakon zabe: Yadda Buhari da Atiku suka fafata a jihohi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa karo na biyu bayan ya doke takwaransa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar. Shugaba Buhari ya samu…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa karo na biyu bayan ya doke takwaransa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Shugaba Buhari ya samu kuri’a 15,191,847, sannan Atiku Abubakar ya samu kuri’a 11,262,978.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da sakamakon bayan

Wakilin PDP a wajen tara sakamakon zaben. Osita Chidoka ya bukaci INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben, bukatar da Shugaban INEC ya ce ba zai yiwu ba, sai dai amma ya ce za su saurari koken kowa daga baya.

Buhari ya lashe jihohi 19, Atiku kuma ya samu jihohi 17.

Shugaba Buhari ne ya lashe jihohin Ekiti da Osun da Kwara da Nasarawa da Kogi da Gombe da Yobe da Neja da Jigawa da Kaduna da Bauchi da Legas da Ogun da Kano da Katsina da Borno da Sakkwato da Kebbi da Zamfara.

Atiku kuma ya lashe jihohin Abia da Enugu da Anambra da Oyo da Adamawa da Edo da Binuwei da Imo da Filato da Taraba da Kuros Riba da Akwa Ibom da Delta da Ribas da Abuja.