✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakamakon Zabe: ‘Yan sanda sun kama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano

Yan sanda sun kama mataimakin Gwamnan kano Dokta Nasiru Yusuf Gawuna saboda tayar da hargitsi a wajen tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nassarawa. Baya ga…

Yan sanda sun kama mataimakin Gwamnan kano Dokta Nasiru Yusuf Gawuna saboda tayar da hargitsi a wajen tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nassarawa.
Baya ga mataimakin Gwamnan rundunar ta cafke Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa Lamin Sani.
Rahotanni sun bayyana cewa ana tsaka da tattara sakamakon zabe ne Mataimakin Gwamnan Kano da wadancan mutane tare da wasu yan bangar siyasa suka yi wa ofishin INEC na karamar hukumar ta Nassarawa tsinke tare da kokarin tayar da hargitsi a wurin.