Search
Subscribe
#Sakamakon Zaben Kogi: APC ta lashe Kananan Hukumomi 10 cikin 15

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello

#Sakamakon Zaben Kogi: APC ta lashe Kananan Hukumomi 10 cikin 15

Dan takarar zaben Gwamnan Kogi na jam’iyyar APC Yahaya Bello, ne ke kan gaba a sakamakon zaben da aka sanar na Kananan Hukumomi 15 cikin 21 da aka sanar. Gwamna Yahaya Bello ya ba abokin takararsa na jam’iyyar PDP Musa Wada, tazarar kuri’u 233,004.

Yahaya Bello na APC ya samu kuri’u 334,474

Musa Wada na PDP ya samu kuri’u 101,470.

Sakamakon na bayyana cewa, APC ta lashe kananan Hukumomi 10. Yayin da PDP ke da kananan hukumomi 5.

Kananan Hukumomin da Yahaya Bello na APC ya lashe sun hada da: Ajaokuta, Adavi, Okene, Ogori Magongo, Olamaboro, Okehi, Mopa Muro, Kabba Bunu, Kogi-Kotonkarfe da Ijumu.

Kananan Hukumomin da Musa Wada na PDP ya lashe sun hada da: Omala, Idah, Igalamela/Odolu, Yagba East da Karamar Hukumar Yagba West.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin