✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakataren Masarautar Kano Mahmud Bayero ya rasu

Za a yi jana'izar Alhaji Mahmudu Aminu Bayero da karfe 2.00 na rana a Kofar Kudu

Sakataren masarautar Kano, Alhaji Mahmud Aminu Bayero ya rasu.

Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya bayana wata doguwar jinya a Asibitin Kashi na Dala dake Kano.

Da yake tabbatar da labarin, daya daga cikin ‘ya’yan mamacin, Ahmad Aminu Bayero ya ce marigayin ya rasu ya bar ‘ya’ya 12 da kuma jikoki da dama.

A cewarsa, marigayin ya shafe sama da shekaru 50 a masarautar kuma ya rike mukamai da dama a cikinta.

“Da farko dai ya rike makamin babban sakataren sarkin Kano, marigayi Ado Bayero daga bisani ya zama sakataren masarautar gaba daya,” inji Ahmad.

An dai gudanar da jana’izar marigayin ne a fadar sarkin Kano dake Kofar Kudu kuma tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.