✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sake bude Kasuwar Ganye da ke Bauchi abin yabo ne – Shugaba

Shugaban Kungiyar ’Yan Lemo da ke Maraba a Jihar Nasarawa kuma Dan Masanin Ganye da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Hussaini Abdullahi…

Shugaban Kungiyar ’Yan Lemo da ke Maraba a Jihar Nasarawa kuma Dan Masanin Ganye da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Hussaini Abdullahi ya yaba da matakin da Gwamnan Bauchi, Barista Mohammed Abubakar ya dauka kwanan nan na sake bude tsohuwar Kasuwar Ganye da ke jihar.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maraba inda ya ce ba sake bude kasuwar zai fadada ya kuma bunkasa harkokin kasuwanci a garin,  a kuma samu ci gaba a garin da jihar baki daya.

“Gwamnan Bauchi ya cancanci yabo idan aka yi la’akari da yadda kasuwar za ta je nesa wajen bai wa ’yan kasuwa a garin damar ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba,” inji shi. Sai ya bukaci sauran gwamnonin kasar nan su yi koyi da abin da Gwamnan ya yi ga ’yan kasuwar.

Ya kuma jinjina wa sarakunan gargajiya na garin Ganye da jihar baki daya a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da Shugaban Jam’iyyar APC na jihar da Shugaban Karamar Hukumar Toro da sauran masu kishin ci gaban garin da jihar baki daya dangane da jajircewa da suka yi wajen bude kasuwar.

Sai ya yi kira ga ’yan kasuwan da ke garin su koma kasuwar don fara amfani da ita su kuma rika kula da kasuwar yadda ya dace don cin moriyarta.