✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon Alka’ida ya haifar da rufe ofisoshin jakadancin Amurka da Turai a Gabas ta Tsakiya

kasashen Amurka da Birtaniya sun rufe ofisoshin jakadancinsu a Gabas ta tsakiya da wasu sassa na Afirka, a sanadiyyar wasu bayananj sirri na i-mail da…

kasashen Amurka da Birtaniya sun rufe ofisoshin jakadancinsu a Gabas ta tsakiya da wasu sassa na Afirka, a sanadiyyar wasu bayananj sirri na i-mail da tarho da sakon rediyon kungiyar alka’ida da aka samu a kasar Yemen. Sakon sirrin ya yi nuni da cewa za a kai hari  wani ofishin jakadanci. Don haka amurka ta umarci ‘yan kasarta da su fice daga kasar. Ita ma Birtaniya ta kulle na ta ofishin.
’Yan majalisar Amurka sun bayyana yadda aka kulla babban makirci, amma ba su yi cikakken bayani ba, sai dai jami’an asirin kasar, sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa akwai yiwuwar ofishin jakadanci daya ake nufin kai wa harin ko kuma wasu da dama da ke da alaka da kasashen Turai. Wannan rahoto dai ya sanya Gwamnatin Obama ta rufe ofisoshin jakadancinta a kasashen da suka hada da Gabas ta Tsakiya da Bangladesh da Gabashin Indiya da Madagascar. Kodayake Amurka ta bude wasu ofisoshin da take da tabbacin suna da kariyar tsaro, wadanda suka hada da na Kabul a Afghanistan da Baghdad a kasar Iraki.
A Afirka kuwa kasashen da aka rufe ofisoshin jakadancinsu, sun hada da Somalia da Mali da Libya.
kasar Jamus ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasar Yemen. Ma’aikatar harkokin wajen Norway, ta takaita ayyukan hulda da jama’a a ofisoshin jakadancinta 15 da ke Gabas ta Tsakiya da Afirka, wadanda suka hada da na kasar Saudiyya.
Wannan sako na alka’ida, ofishin Mai bayar da shawara kan harkokin tsaron Amurka da Hukumar Asiri ta CIA suka tattara bayanan sirri daga sakonnin kungiyar Alka’ida.