Sakon Bagizagen Mako

Muntaqa Abdulhadi Dabo, tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya
Muntaqa Abdulhadi Dabo, tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya

Bakonmu na wannan makon, shi ne tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Muntaka Abdulhadi Dabo (08036397682), Sardaunan A Bari Ya Huce, Zariya. Ko mene ne sakon tsohon Shugaban na Gizagawa? Ga abin da yake cewa:

Assalamu alaikum, Gizagawa! Gizagawa! Gizagawa!!!

Ina kira gare mu da mu, jajirce mu ci gaba da ba da hadin kai da goyon baya ga shugabannin kungiya; domin samun sauke nauyin da ke kansu.

A zahirin gaskiya mun yi sanyi kan hidimar kungiya da muke yi, ba kamar shekarun baya ba. Wai shin ina Gizagawan suke ne?  Me ya sa muka fara barci? So muke zumuncin da muka assasa da aikin alherin su wargaje a dare daya?

Ya kamata mu farka daga barcin da muka fara yi, in dai muna so mu ci gaba da aikin da muka faro a baya. Saboda haka ina kira a gare mu, da mu hada karfi da karfe domin ganin wannan kungiya ta kai ga inda ake bukatar ta kai.

ADVERTISEMENT

Muna ganin yadda Mai girma Shugaba na Kasa, Malam M. K. Adam Gombe da ’yan majalisarsa suka jajirce wajen ganin an farfado da ayyukan da aka saba yi. Don haka mu yi kokari mu ba su dukkan hadin kai da suke bukata, domin kai mu ga tudun-tsira da kuma samun damar gudanar da taron kasa.

Jinjina ta musamman ga Madugu Uban Zumunci, Malam Bashir Yahuza Malumfashi da yake hidima da mu tare da ayyukan kungiya ba dare ba rana. Allah Ya kara daukaka, amin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya